ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, August 3, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

by Muhammad
1 year ago
Adamawa

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Adamawa ya karu zuwa 23.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda suka rasu a ibtila’in da ya auku a ranar Lahadi.

  • Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa
  • Adamawa Ta Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na ₦70,000 Ga Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi 

Gwamnan ya nuna damuwarsa da alhini matuƙa bayan ganawa da waɗanda ambaliyar ta rutsa da su, yana mai cewa irin wannan al’amari mai muni bai taɓa faruwa ba a baya ba.

ADVERTISEMENT

Ambaliyar ta faru ne da misalin ƙarfe 1 na safiyar Lahadi a sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi, wanda ya haddasa mutuwar mutane 23 da kuma lalata dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Yayin jawabi ga waɗanda abin ya shafa a sansanin wucin gadi da aka kafa a Kwalejin Aliyu Mustafa, Yola, Gwamna Fintiri ya sanar da kafa kwamitin na musamman don tantance adadin asarar da aka yi.

LABARAI MASU NASABA

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu.

Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya.

Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa.

Adamawa
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
  • Muhammad
    Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100
  • Muhammad
    ‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
  • Muhammad
    Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi

MASU ALAKA

DSS
Manyan Labarai

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

August 3, 2026
Zamfara
Labarai

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

August 3, 2026
Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga
Manyan Labarai

Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

August 3, 2026
Next Post
An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

LABARAI MASU NASABA

DSS

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

August 3, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran

Iran Ta Musanta Iƙirarin Trump Kan Sabbin Tattaunawa da Amurka

August 3, 2026
Zamfara

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Shida, Sun Sace Mutane 75 A Zamfara

August 3, 2026
Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

August 3, 2026
Kamfanin Abinci Na ‘BUA Foods’ Ya Samu Ribar ₦292.27bn A Rabin Farkon 2026

Kamfanin Abinci Na ‘BUA Foods’ Ya Samu Ribar ₦292.27bn A Rabin Farkon 2026

August 3, 2026
Adamawa

WAFCON 2026: Ƴan Wasan Nijeriya 2 Ba Zasu Buga Wasan Ƙarshe Na Rukunin C Ba

August 2, 2026
Babban Bankin Sin: Za A Ci Gaba Da Gudanar Da Matakan Saukaka Harkokin Kudade

Babban Bankin Sin: Za A Ci Gaba Da Gudanar Da Matakan Saukaka Harkokin Kudade

August 2, 2026
Yawan Tikitin Kallon Fina Finan Sin Da Aka Sayar A 2026 Ya Zarce Yuan Biliyan 23

Yawan Tikitin Kallon Fina Finan Sin Da Aka Sayar A 2026 Ya Zarce Yuan Biliyan 23

August 2, 2026
Adamawa

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Ceto Mutane 9 A Zamfara

August 2, 2026
Sin Ta Fitar Da Shirin Shekaru 5 Na Daukaka Tsarin Tallata Da Samar Da Kayayyaki Domin Kyautata Hidimomi A Kauyuka

Sin Ta Fitar Da Shirin Shekaru 5 Na Daukaka Tsarin Tallata Da Samar Da Kayayyaki Domin Kyautata Hidimomi A Kauyuka

August 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.