Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Honorabul Isa Ashiru Kudan, ya kai ziyarar tare da neman goyan baya ga Malamai da Ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), kan kudurinsa na neman kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.
An gudanar da taron a babban dakin taro da ke Cibiyar Aikin Gona na jami’ar.
- Tinubu Ne Kadai Zai Iya Magance Rashin Tsaro Da Tabarbarewar Tattalin Arziki – BuhariÂ
- Babu Gaskiya A Labarin Cewar G-5 Ta Goyi Bayan Takarar Atiku – Samuel Ortom
Taron ya samu halartar manyan Farfesoshi, Daktoci da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.
Shugaban taron, Dakta Hamisu Lawal, ya ce dan takarar nasu na neman goyon bayan jama’a a matsayinsa na mai son ya jagoraci al’umar Jihar Kaduna.
Shugaban ya kara da cewa ma’aikatan Suna son kuma su mika tambayoyin da suka shafi kujerar da yake nema don samun fahimtar juna tare da shifida tafiya mai tsafta a tsakanin al’umar dake jihar Kaduna baki daya.
Farfesoshi ne da manyan yan Boko da gogaggun yan siyasa suka halacci wannan taro
Honorabul Isa Ashiru ya saurari tambayoyi daga mahalatta taron wanda suka shafi kudirin da ke kare mutuncin al’umma kamar maganar kalubalen da harkar Ilmi ke fuskanta a halin yanzu, da kuma maganar tabarbarewar da harkar tsaro dake kara girma a halin yanzu sai maganar jin dadi da walwalar ma’aikata da komi ya lalace a jihar ta Kaduna.
Hakazalika, ya ce Ashiru ba shi da wani buri face sauya fasalin jihar, ta hanyar shimfida ayyukan more rayuwa da jina al’umma.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, godiya ya yi ga dubban ma’aikatan jami’ar bisa yadda suka nuna kauna ga dan takarar nasu, inda ya ce da ikon Allah PDP ba za ta bai wa jama’a kunya ba.
Dan takarar gwamnan na PDP, Ashiru, ya bayyana jib dadinsa kan yadda ma’aikatarln suka yi masa dafifi don nuna goyon bayan takararsa.
“Na ji dadi sosai kuma na samu kwarin guiwa a tafiyarmu a jiha da kasa baki daya.”
Ashiru na PDP zai kara da Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris, 2023.