Dan majalisar wakilai, Shamsudden Danbazau, ya ce alamu sun nuna cewar Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC zai doke sauran ‘yan takara domin lashe zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.
- DSS Ta Saki Doyin Okupe Bayan Tsare Shi
- Ɗan China Da Ake Zargi Da Kisan Ummita Ya Ce Naira Miliyan 60 Ya Kashe Mata
Danbazau, wanda da ne ga Abdululrahman Danbazau (mai ritaya), tsohon babban hafsan sojin Nijeriya, ya ce tsohon gwamnan Jihar Legas, yana da abin da ake bukata don juya kasar nan.
“Tinubu yana da gogewar da zai fitar da kasar daga halin da take ciki. Shi ne mutumin da yake da gogewar kula da duk wadannan batutuwan da suka shafi ‘yan Nijeriya; zai hada kasar waje daya tare da kawar da tashin hankali da ake fuskanta,” in ji shi.
Ya ce jam’iyyar APC ta riga ta lashe zaben 2023.
Danbazau ya ce an gwada APC kuma an gano cewa tana da gogewa a kasar nan.
“Tinubu shugaba ne mai basira, ba zai yi kasa a gwiwa wajen ganin komai ya saitu a kasar nan,” in ji shi.
Da yake magana kan kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta, Danbazau, ya ce Nijeriya ta samu ci gaba, inda ya ce ana amfani da jirage marasa matuka, lamarin da ya sanya abubuwa suka fara daidaita.
“Muna bukatar samun karin taswirar kasa na musamman, inda za mu iya aika jirage marasa matuka don kai wa ‘yan ta’adda hari a kowane lungu na kasar nan.
“Daga shekarar 2014 zuwa 2018 na ki zuwa sallar Juma’a saboda tsoron harin bam. Dole ne na kasance a gida ko kuma na salla a bariki, amma tun shekara ta 2016, na soma halartar sallar jam’i a masallatan jama’a.
“An magance kalubalen tsaro kuma za ku ga abin da shugaban kasa ke yi ta hanyar zuba jari mai yawa, samun jiragen sama marasa matuka, yin bincike da tura jami’an sojojinmu zuwa wasu kasashe don koyo dabaru da magance matsalolin tsaro,” in ji shi.
Danbazau ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta yi abun a zo a gani a fannin tsaro.