Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi barazanar cewa, duk wanda ya yake shi a kan takararsa a Jihar Kano a 2023, zai gane kurensa.
A kwanan nan ne dai, aka ruwaito gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ya shaida wa magoya bayansa a jihar cewa, Kano za ta sake maimaita abin da ya faru, a zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar a 1993, inda Kano ta mara wa marigayi MKO Abiola ta ki mara wa abokin takararsa, marigayi Bashir Tofa, inda hakan ke nuna ‘yar manuniya ta samarwa da dimbin kuri’u ga Tinubu sama da Kwankwaso.
- Alluran Riga-Kafin COVID-19 Na Kasar Sin Na Da Tsaro Da Inganci
- Kotu Ta Fara Sauraren Shari’ar Raba Auren ‘Yar Ganduje A Kano
Kwankwaso a martaninsa bayan ‘yan kwanaki da jawabin Ganduje, ya ce a kwanan baya na gudanar da gangamin yakin neman zaben na wanda ya kasance yafi sauran gangamin da na gudanar.
Ya ce, na yi wani gangamin a Wudil da kuma yin wani, a Bichi na kuma bude ofis dina na yakin neman zabe a kano ta tsakiya.
A cewarsa, a yanzu bani da lokacin yin nagana akan wancan mutumin domin ban san ko ya furta wannan maganar ko bai furta ba.
Kwankwaso ya kara da cewa, amma a zahirance duk wanda ya yake ni a takara ta, zai gane kurensa.
Ya ce, duk wanda ya sanni ya kuma san tarihi na, in na lashe zaben Kano ma za ta amfana da shugabanci na, haka arewa da kuma Nijeriya baki daya.
Kwankwaso ya ce, na yi mamakin da wani ke cewa inje in yi gamgami a Kano bayan na san na yi gangamin da dama a jihar, mussman wadanda na gudanar a watannin dismaba da na janairu da kuma wadanda na yi a mazabu uku na jihar.