Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na kira ga kasashen Amurka da Japan, da su kauracewa tunanin cacar-baka, da akidun nuna wariya, su kuma dakatar da kirkirar wasu makiya na jabu, da rura wutar yakin cacar-baka a yankin Asiya da Fasifik, kana bai dace su kasance masu gurgunta yanayin daidaito da ake da shi a yankin Asiya da tekun Fasifik ba.
Wang Wenbin, wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Jumma’a, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da sanarwar hadin gwiwar kasashen biyu, ya ce rahotanni sun tabbatar da cewa, cikin waccan sanarwa ta Amurka da Japan, kasashen 2 sun kira Sin “Babbar kalubale a yankin tekunan Indiya da Fasifik, da ma karin wasu yankunan”. Sanarwar ta kuma soki kasar Sin, don gane da manufofin ta game da yankin Taiwan, da Hong Kong, da jihar Xinjiang, da ma manufofin kasar masu nasaba da teku.
Wang, ya ce Amurka da Japan, na cewa suna tallafawa zaman lafiya da tsaron shiyyoyi, amma a zahiri suna lalubo hanyoyi ne na gina tsarin girkewa, da amfani da karfin soji. Kaza lika suna cewa burin su shi ne samar da yanayin gudanar da harkoki a bude, a yankin tekunan Indiya da Fasifik, amma kuma abun da suke yi shi ne, kafa tsarin rarraba kawuna, da haifar da fito na fito. (Saminu Alhassan)