Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya sanar da shirin fara hakar man fetur a Jihar Nassarawa a cikin watan Maris mai zuwa wanda ke matsayin karon farko da aka gano irin wannan albarkatu a jihar ta Arewacin kasar nan.
Matakin gano rijiyar man a Nasarawa dai na zuwa ne a wani yunkuri da NNPC ke yi don lalubo sauran sassan kasar nan da ke da irin wannan albarkatun karkashin kasa a cikin Nijeriya.
- Bai Dace Amurka Da Japan Su Zamo Masu Wargaza Zaman Lafiya A Yankin Asiya Da Fasifik Ba In Ji Jami’in Kasar Sin
- Gwamnatin Zamfara Ta Gano Likitocin Bogi 199 A Jihar
NNPC karkashin jagoranci Mele Kyari, na ci gaba da baza koma don lalubo man fetur a kan tsaudari sabanin cikin ruwa da a baya kasar nan ke lalube a yankin kudanci.
Lokacin da ya ke karbar bakoncin tawagar wakilcin al’ummar ta Jihar Nasarawa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule a hedikwatar kamfanin na NNPC da ke Abuja, Kyari ya bayar da tabbacin cewa kamfanin zai jagoranci aikin hakar man cikin watan Maris mai zuwa.
A watan Nuwamban bara ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar man fetur a jihohin Bauchi da Gombe shekaru biyu bayan sanar da gano albarkatun man a jihohin biyu na Arewacin Nijeriya irinsa na farko a tarihin kasar nan.