Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta yaye jami’ai dubu ɗaya da ɗari takwas daga Makarantar Horas Da Jami’an Shige da Fice ta Kano (ITSK) da kuma Kwalejin Horaswa ta Hukumar Kwastam (CTC).
Jami’an da aka yaye waɗanda da suka yi kwas na 23 na share fage, an yaye su ne a makarantar ta ITSK ranar Asabar 14 ga Janairun 2023.
Da yake jawabi, Shugaban NIS, Isah Jere Idris ya taya waɗanda aka yaye murna tare da yin kira a gare su, su yi cikakken aiki da horon da suka samu bisa dokoki da ƙa’idojin aiki na hukumar.
CGI Isah Jere wanda Mataimakin Kwanturola Janar, mai kula da sha’anin ma’aikata, Babangida Usman ya wakilta tare da duba faretin waɗanda aka yaye, ya bayyana cewa, mahukuntan hukumar na yanzu na ci gaba da duƙufa ka’in da na’in wajen inganta sha’anin jami’ai ta hanyar horaswa domin samar da ƙwararrun jami’ai da za su iya fuskantar ƙalubalen da ke tasowa a ɓangaren kula da tsaron iyakokin ƙasa da harkar shige da fice.
CGI Isah Jere ya kuma nanata buƙatar da ake wa jami’an su kauce wa sakaci da zubar da mutuncin aikin musamman yanzu da ake fuskantar zaɓen 2023, kana ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci komawa ‘yar gidan jiya ba. Ya buƙace su, su kasance ‘yan ba ruwana tare da tabbatar da cewa babu wani baƙo ɗan ƙasar waje da aka bari ya shiga cikin harkokin zaɓen.
Ya bayyana cewa, yaye ɗaliban na wannan karon ya kafa tarihi a NIS domin ba a taɓa samun adadin waɗanda hukumar ta horas da suka kai wannan adadin ba a lokaci guda. Ya jinjina Wa kwamandojin Makarantun horaswa na ITSK da NITSOL bisa tsara horaswar kamar yadda ya kamata.
CGI Isah Jere ya kuma gode wa Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da Gwamnatin Tarayya bisa goyon bayan da suke ci gaba da bai wa hukumar a ayyukanta tare da ƙara yawan jami’ai.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, Tony Akuneme ta yi ƙarin hasken cewa, cikin manyan baƙin da suka halarci bikin har da jakadan Nijeriya a Benin da Jakadan Nijeriya a Nijer, da Kodinetan Shiyya ta Biyu, Kwamandan Birget ta 3 da ke Kano da sauran manyan jami’an Gwamnatin Kano da sauran wakilan rundunonin tsaro da ke jihar.