Shugaban Kungiyar fafutukar neman zaben Bola Ahmad Tinubu (Tinubu Support Organisation) a Jihar Kano, Alhaji Yusuf Yunusa Bakin- Zuwo ya bayyana cewar dan takarar na jam’iyyar APC ne mafi cancanta da dacewar Shugabancin Nijeriya a 2023.
A cewarsa tsohon Gwamnan na Jihar Lagas nagartaccen dan siyasa ne wanda ke da kwarewa da gogewar shugabanci, sanin ciki da wajen matsalolin al’umma, lakantar hanyoyin magance su da sanin makamar iya hada kan kasa da fahimtar juna a tsakanin addinai.
Bakin- Zuwo wanda kuma fitaccen dan kasuwar Kasa da Kasa ne ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai a Sakkwato a rangadin tallata takarar Tinubu yana cewar a kungiyar TSO a karkashin jagorancin Shugabanta na Kasa (DG) Hon. Aminu Sulaiman su kan shiga lungu da sakon Kasar nan domin yada kyawawan manufofi da kudurorin Tinubu ga al’ummar Kasar nan sama da kowace kungiya.
Ya ce “Nijeriya na bukatar hazikin gwarzon shugaba mai gaskiya da adalci wanda zai bunkasa tattalin arziki, inganta haraji, habaka kasuwanci, fitowa da hanyoyin rage dogaro da man fetur, karawa Jihohi kason wata- wata na Gwamnatin Tarayya da uwa uba kammala hobbasar kwazon Shugaba Buhari wajen kawar da matsalolin tsaro da yaki da ta’addanci.”
Ya kara da cewar “Gagarumar karbuwar da Jagaban ya samu daga Arewaci da Kudancin Kasar nan babbar alama ce ta samun nasararsa ta zama Magajin Shugaba Buhari ta hanyar yi wa jam’iyyun adawa bugun ‘ya’yan kadanya wanda muna da tabbacin a budadden mulkinsa za a samu yadda da aminci a tsakanin Gwamnati da wadanda ake mulki.”
“Idan a na maganar karbuwa Tinubu a Nijeriya, Kano ba a ma maganarta domin 100 bisa 100 Kanawa za su zazzaga masa ruwan kuri’u kuma kowa ya san tasiri da girman kuri’un Kano a siyasar Nijeriya, hatta nan Sakkwato da take Jihar PDP, kuma Jihar shugaban yekuwar neman zaben PDP, za mu ba Atiku da Tambuwal mamaki in sha Allah.” In ji shi.
A cewar Bakin- Zuwo, Tinubu jagora ne nagari mai kima da tasiri, mai fada da cikawa wanda a kodayaushe ci- gaba da bunkasar al’umma shine burinsa don haka zabensa a matsayin Shugaban Kasa zabe ne na gina kasa, inganta jin dadi da walwalar jama’a, yaki da fatara, bunkasa noma da kiyo, inganta wutar lantarki, farfado da masana’antu, bunkasa hanyoyin kirkirar sababbin abubuwa ta hanyar inganta kimiya da fasaha da shigowar masu zuba jari tare da magance matsalolin ilimi da kiyon lafiya tare da shayar da al’umma romon mulkin Dimokuradiyya a dukkanin matakai.