Hukumar jami’an tsaro ta DSS, ta karyata rahoton cewa, jami’anta sun yiwa shalkwar babban bankin Nijeriya CBN da ke Abuja kawanya domin su kama gwamnan babban bankin Godwin Emefiele a ranar litinin.Â
A cikin sanarwar da kakakin DSS Peter Afunaya ya fitar ya danganta rahoton a matsayin na karya da kuma son karkatar da kan ‘yan Nijeriya.
Ya ce, rahoton na karya akan kamun wanda aka wallafa shi a yau 16 ga watan janairu 2023 cewar, jami’an hukumar sun shiga hedkwatar don kama Godwin, karya ce tsagwaron ta.
A wani bangaren kuma, rahotonni sun nuna cewa, gwamnan bankin, Godwin ya dawo Nijeriya bayan kammala hutunsa na shekara da ya yi a kasar waje.
Godwin dai, ya tafi hutun ne, a watan Disambar 2022, inda kuma ya dawo bakin aiki a yau 16 ga watan janairu.
Da Dumi-Dumi: Na Dawo Zan Ci Gada Da Yin Ayyuan Da Buhari Ya Umarce Ni- Emefiele
Gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele,ya shelanta cewa ya dawo gida Nijeriya kuma a shirye yake ya ci gaba da gudanar da ayyukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarce shi da yi.
Godwin a cikin wata sanarwar mai taken gwamnan CBN ya dawo kan aikisa da karfin guiwa bayan kammala hutunsa na shekara.
Babbar kotun da ke Abuja a watan 2022 ne ta dakatar da DSS daga yinkurinta na kama Godwin biyo bayan zargin sa da hannu a daukar nauyin aikata ta’addanci a kasar nan.