Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, gwamnatin kasar ta yi wa matakanta na kandagarki da dakile annobar cutar COVID-19 gyaran fuska, bisa yanayi da kuma lokacin da ake ciki, wanda shi ne mafi dacewa domin matakan kandagarkin da na raya tattalin arziki da zaman takewa su dace da juna yadda ya kamata.
Ya ce yayin da yanayin cutar a kasar Sin ke ingantuwa, kuma harkokin samar da kayayyaki da na yau da kullum suka yi saurin komawa kamar yadda suke a baya, za a gane irin cikakken kuzari da damarmakin da tattalin azrikin Sin ke da shi, wanda zai kara tabbaci da karfi ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
A jiya Litinin ne sakatare janar na hukumar hadin gwiwar raya tattalin arziki da samun ci gaba (OECD), Mathias Cormann ya bayyana cewa, yana maraba da daidaita matakan kandagarkin annobar da Sin ta yi, wanda zai taimaka wajen tabbatar da gudanar harkokin samar da kayayyaki da saukaka hauhawar farashin kayayyaki a duniya. (Fa’iza)