Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (BOSEMA), ta bayar da tallafin kayan abinci na miliyoyin nairori ga ‘yan gudun hijira na Gubio da ke garin Maiduguri.
Da take mika kayyakin ga shugabanin sansanin ‘yan gudun hijirar, Daraktar hukumar BOSEMA, Hajiya Yabawa Kolo, ta ce, an bayar da kayan tallafin ne don rage radadi ga ‘yan gudun hijirar ne da iyalansu’.
- An Kashe ‘Yan Bindiga 4 Da Cafke Matar Da Ke Kai Wa ‘Yan Ta’adda Makamai A Kaduna
- Kotu Ta Daure Wata Mata Shekara 30 Saboda Ta Yi Bari
Ta kuma kara da cewa, kayayyakin da aka bayar sun hada da buhuna masara 400, buhun wake 50 da man girki katan 50 da kuma katan magi 30.
Ta ce, gwamnati na fatan kayan abinci zai matukar taimaka wa rayuwar ‘yan gudun hijirar musamman ganin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Shugabar ta kuma bayyana cewa, an samu kayan agajin ne daga hukumar bayar da agajin abinci ta duniya ‘World Food Programme’ da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA).
Daga nan ta ce, rashin kudi ne ya sanya watan shida kenan dasu bayar da agaji ba ga ‘yan gudun hijirar,
Ta kuma nemi su kara hakuri, da yardar Allah abubuwa za su gyaru nan gaba kadan.
A kwai ‘yan gudun hijira daga kananan hukumomi 9 a sassanin na Gobio.