Mataimakiyar shugaban kasar Uganda Jessica Alupo, ta jinjinawa kasar Sin, bisa tallafin da take baiwa kasashe masu tasowa, karkashin tsarin hadin gwiwar su.
Jessica Alupo ta bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin da take jawabin bude babban dandalin kasashen Afirka na 2, na hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da sassa 3 game da wanzar da ci gaba mai dorewa.
Yayin taron na yini 3 wanda aka bude a birnin Kampala fadar mulkin kasar ta Uganda, uwar gida Alupo, ta ce Sin na marawa kasashen Afirka ciki har da kasar Uganda baya, a fannonin gina hanyoyi, da samar da ababen more rayuwa masu nasaba da makamashi. Kaza lika Sin ta samar da kudaden gina manyan tashoshin samar da lantarki ta ruwa a Karuma da Isimba duka a kasar ta Uganda.
Alupo ta kara da cewa, karkashin asusun shirin bunkasa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin samar da abinci, da raya ayyukan gona ko SSC, an yi nasarar kyautata rayuwar dumbin al’ummar Uganda, ta hanyar bunkasa yabanyar da suke samu.
Jami’ar ta kara da cewa, baki dayan manufar taron ita ce samar da kwarewa, da dabarun jurewa dukkanin kalubalen ci gaba tsakanin kasashe masu tasowa, ta yadda za su iya warware kalubaen ci gaba gwargwadon burikan su, da akidu, da bukatun su na kashin kai.
Taken taron na wannan karo shi ne “Gina kwarewar kasa game da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da na sassan 3 a nahiyar Afirka, da gina kawance domin samar da al’umma mai juriya da wanzuwar ci gaba. (Saminu Alhassan)