Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Alhamis cewa, kasar Sin na shawartar Amurka cewa, yunkurinta na toshe kofofin wasu kasashe, na nufin toshewa kanta hanya.
A kwanan nan ne mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin kungiyar Tarayyar Turai, Valdis Dombrovskis, ya ce Amurka da Turai sun fara tattaunawa game da dokar Amurka kan rage hauhawar farashin kayayyaki.
A cewar Wang Wenbin, tabbas, tsarin Amurka na rashin daidaito wajen bayar da tallafi ko kuma bin bashin haraji, zai haifar da matsaloli.
Ya jaddada cewa, kamata ya yi takara ta kasance bisa gaskiya da sanin ya kamata. Yana mai cewa yunkurin Amurka na danne ‘yancin wasu kasashe na samun ci gaba ta hanyar yin gaban kanta wajen daukar matakai na kashin kai da kariyar ciniki, sam bai dace ba, kuma ya saba ka’idojin kasuwa da na raya tattalin arziki, haka kuma ba zai yi nasara ba. (Fa’iza)