A daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zaben 2023, wanda aski ya zo gaban goshi, kowane dan takarar shugaban kasa ya kara matsa kaimi domin tallata manufofinsa ga ‘yan Nijeriya, inda a wannan makon abin ya kara zafi har ta kai ga manyan ‘yan takarar sun shafa wa junansu kashin kaji da nufin dusashe tauraron juna.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gargadi ‘yan Nijeriya a kan kar su sake su zabi PDP a zaben 2030, inda ya ce dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar dan rashawa ne da yake da kudirin sayar da Nijeriya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki Ba
- Me Sin Ta Kawo wa Duniya Cikin Shekaru 3 Da Ta Shafe Tana Kokarin Tinkarar Cutar COVID-19
Tinubu ya bayyana haka ne a lolacin gangamin yakin neman zabensa a garin Ilorin da ke Jihar Kwara a tsakiyar makon nan.
Har ila yau, kwamitin yakin neman zaben APC ya bukaci a cafke tare da gurfanar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zarge shi lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasa a tsakanin 1999 zuwa 2007, inda ya hada baki da mai gidansa a lokacin, Cif Olusegun Obasanjo, wajen sace dokiyar kasa ta amfani da sayen motoci na alfarma.
Kwamitin yakin neman zaben APC ya bukaci jami’an tsaro da su yi gaggawar damke Atiku tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa kashe kudin kasa wanda ya yi amfani da sunayen kamfanoni masu rajista lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasa.
Mai Magana da yawan kwamitin yakin neman zaben APC, Festus Keyamo ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, wanda ya kasance tare da sauran mambobin tawagar yada labarai na kwamitin.
Kwamitin ya zargi Atiku tare da maigidansa, Obasanjo wajen kwashe kudin kasa ta hanyar amfani da sayen motoci na musamman.
“Manufar ita ce, an karkatar da kwangilolin gwamnati ga wadansu kamfanoni, sannan aka biya makudan kudade ga wadannan kamfanoni, kuma aka yi amfani da kudaden wajen tallata PDP da gudanar da harkokin kasuwanci na kashin kai da kuma tafiyar da harkokin iyalai.
“A kan wannan lamari, bai kamata bangaren shari’a ya yi gum ba tare da daukan matakan da suka dace cikin ‘yan kawanaki kalilan masu zuwa, domin fara gudanar da shari’ar da ke nema a hana Atiku Abubakar takarar bisa wadannan kwararan hujjoji.
“A bayyane yake yana da kalubale na rashin da’a da cin zarafi da ofishi mafi girma a kasar nan,” in ji kwamitin.
Har ila yau, a wata takardar koke da aka kai wa shugabannin hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annatin (EFCC), hukumar yaki da cin hanci da rashawa da hukumar da’ar ma’aikata (CCB), Keyamo ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su kama Atiku cikin sa’o’i 72, bisa laifukan da ake zarginsa na keta ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, halatta kudin haram, cin amana da cin hanci da rashawa da kuma hada baki.
Tinubu Tsohon Dan Fursuna Ne, Ya Janye – PDP
Da take mayar da martani, PDP ta siffanta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da tsohon dan fursuna da aka hukunta bisa aikata manyan laifuka, inda ta baukace shi ya gaggauta janye takarar shugaban kasa.
Mai Magana da yawun jam’iyyar ta PDP, Debo Ologunagba ya ce abun mamaki ne a ce mutum kamar Tinubu wanda ba za a iya kirga ayyukan damfararsa ba, wadanda suka hada da karya, amfani da jabun takardu, wawushe baitul mali, cin hanci da rashawa da kuma laifuka da suka shafi hukuncin kisa, amma shi ne yake yunkurin cin mutumcin dan takarar shugaban kasa na PDP.
“Sakamakon hukuncin da aka yanke da kuma kwace makudan kudade wadanda suka kai Dala 460,000 daga hannun Tinubu ya tabbatar da cewa bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kuskurima ya tanada.
“Bayan an yanke masa hukunci da kuma cin tararsa na laifin fataucin miyagun kwayoyi a karar da aka shigar bisa karya ka’idojin Amurka, Asiwaju Tinubu bai kamata ya tsaya takara ba, saboda sashi na 137 (1) (d) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa garan bawul ta hana shi zama shugaban Nijeriya.
Haka kuma, shi ma mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya bukaci a kama Tinubu tare da yi masa tambayoyi bisa zarginsa da kafa wata kungiya mai suna ‘Jagaban Army’.
Ya yi zargin cewa kungiyar ta Jagaba Army tana nufin tarwatsa zaben 2023 da kuma kai farmaki a rumfunan zabe domin Tinubu ya samu kuri’u masu yawa.
Ya ce wannan mataki cin zarafi ne ga rundunar sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da kuma karya ‘yancin kasa.
A cewar Ologbondiyan, “Abin takaici ne Tinubu har zai iya kafa sojojin gona domin yin zagon kasa ga harkokin zabe da kuma tsaron kasarmu.
“Kamfen dinmu ya tabbatar da cewa wannan muguwar tafiya ta APC ta Tinubu/Shettima ba zai yi tasiri ba, domin kuma matsayin jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa ba za su taba zaben Tinubu da mataimakinsa Shettima ba wajen shugabancin al’umma ta hanyar da ba ta dace ba tare da yin amfani da sojojin Jagaba.
“Kungiyar Jagaban Army wani shiri ne na kawo ‘yan daba a karkashin jam’iyyar APC tare da mayar da su ‘yan bindigar da za a yi amfani da su wajen tayar da tarzoma a ranar zabe.”
APC Da PDP Sun Ci Amanar ‘Yan Nijeriya Tsawon Shekara 24 – Kwankwaso
Shi kuwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar APC da PDP sun riga sun ci amanar ‘yan Nijeriya na tsawon shekara 24 a karkashin wa’adin mulkinsu.
Kwankwaso ya ce duka jam’iyyun guda biyu sun gaza wajen magance tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa da hada kan ‘yan Nijeriya da dai sauransu. Ya bukaci ‘yan Nijeriya sun kaurace wa jam’iyyun biyu tare da zaban NNPP a zaben 2023.
Ya bayyana hakan ne wurin yakin neman zabensa a yankin arewa ta gabas wanda ya gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Ya yi alkawarin cewa NNPP za ta gyara kurakuran APC da PDP na tsawon shekaru 24.
Ya ce, “Wannan wata dama ce ta tunatar da dukkan wadanda ke nan da kuma wadanda suke sauraro a gida da su ci gaba da mara wa jam’iyyarmu ta NNPP baya.
“Mun tabbatar da cewa wadannan jam’iyyu guda biyu da suka kwashe shekaru 24 suna mulki, sun gaza ta fuskar tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da hadin kan ‘yan Nijeriya.
“Domin haka, mun yi imanin cewa wannan jam’iyyar ita ce kawai amsar gazawar da muka shiga ciki na tsawon shekaru 24 a kasar nan.
“Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar kasancewa a cikin jam’iyyar NNPP, amma muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa jam’iyyarmu ita ce mafita ga wadannan matattun jam’iyyu guda biyu PDP da APC.”
PDP Da APC Danjuma Ne Da Danjummai – Obi
Bugu da kari, shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ba a bar shi a baya ba wajen caccakar manyan jam’iyyun biyu inda ya bayyana cewa PDP da APC danjuma ne da danjummai.
Obi ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, inda ya ce APC da PDP duk gazawarsu iri daya ce.
Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala jawabi a Zauren Chatham Hause da ke Kasar Ingila.
A cewarsa, tsarin da Obi ya zo da shi ya dace da Nijeriya kuma shi ne hanyar da zai iya bunkasa yankin Afirka ta yamma. Domin haka, ya sha alwashin gudanar da kyakkyawan tsari idan aka zabe shi a wata mai zuwa.
Ya dai yi magana ne kan jawabin Obi na Chatham House a gidan talabijin din Channels a wani shiri na siyasa da aka gabatar a ranar Litinin da ta gabata, Okonkwo ya caccaki manyan jam’iyyu da ke takama sun gudanar da wani tsari.
“Shugabana ya yi magana game da lalata tsari, sannan ni da ku mun san cewa wadannan jam’iyyu wato PDP da APC sun gaza bai kamata su shiga takara ba.
“Abin da APC ke cewa a kan PDP gaskiya ne. Sannan abin da PDP ke fadi kan APC gaskiya ne. Abin da APC ke cewa a kanta karya ce. Abin da PDP ke cewa a kanta karya ce,” in ji Kakakain LP.
Da Yuwuwar Zaben Shugaban Kasa Ya Kai Zagaye Na Biyu – INEC
Sai dai kuma, yayin da manyan ‘yan takarar suke ci gaba da gwabzawa a fagen yakin neman zabe, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa akwai yiwuwar zaben shugaban kasa wanda za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ya kai zagaye na biyu.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a Chatham Hause da ke Kasar Ingila. Ya ce INEC a shirya tsaf na gudanar da zagaye na biyu ko da ba a samu wanda ya yi nasara ba a zagayen farko ba.
Da yake magana kan zaben 2023 da shirye-shirye da tabbatar da daidaito, Yakubu ya ce tun shekaru da dama INEC take shiryawa na yiwuwar ko zaben shugaban kasa zai kai zagaye na biyu tun shekaru uku da suka gabata da kuma zaben shugaban kasa na bara.
Ya ce, “Gaskiyar magana ita ce a duk babban zabe hukumar takan shirya. Akalla a wasu lokutan a zabuka na karshe, muna shirye-shiryen yiwuwar hakan.
“Dalili kuwa shi ne har sai an yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima, domin kuwa mako guda ne kawai ake yin zaben shugaban kasa a zagaye na biyu idan har hakan ta faru.
“Yawan adadin wadanda suka yi rajistar zabe da muke da su, ba zai yiwu a buga takardun jefa kuri’a da na sakamakon zabe da ake bukata ba kuma har a kai su wurare da za a gudanar da zabe.
“Dokin haka, duk zabuka guda uku da suka gabata, muna yin tanadin yiwuwar zaben shugaban kasa idan har hakan ta faru. Idan hakan ta faru, to ba za mu samu wata matsala ba kuma a wannan shekarara lamarin bai sha bamban ba.”
Ya ce sakamakon gyara kundin tsarin mulki da aka yi, a yanzu haka INEC makonni uku kacal take da su a tsakanin zaben shugaban kasa da kuma zabe zagaye na biyu.
Ya ce bayanai da aka samu sun nuna cewa Nijeriya na da yawan masu kada kuri’a miliyan 16.7 fiye da sauran kasashen yammacin Afirka.
Yakubu ya tabbatar wa masu zabe cewa na’urar tantance masu kada kuri’a tana nan daram, ya ce za a yi amfani da ita ne domin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Ya yi nuni da cewa, zaben 2023 zai kasance zakaran gwajin dafi a kasar nan, yana mai jaddada cewa kuri’un da aka kirga a lokacin zabe ne kadai za su tabbatar da wanda ya lashe zaben.
Yakubu ya ce zaben zai kasance aikin hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki, ya kara da cewa hukumarsa ta nuna haka a zaben da suka shude.