A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Nijeriya ta kwato yankuna daga hannun ‘yan ta’adda ta hanyar zuba jarin sama da Dala biliyan 1 (N445bn na kasuwanci ko kuma Naira biliyan 740 a kasuwar bayan fage) domin sayo makamai daga Amurka da sauran kasashe kawaye domin ci gaba da yaki da ayyukan da ta’addanci tun daga 2015.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron zaman lafiyar Afirka na 2023, da aka gudanar a Nouakchott, Jamhuriyar Musulunci ta Mauritania.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki Ba
- Tabarbarewar Aikin Gwamnati A Matakin Jihohi
Shugaba Buhari wanda taron zaman lafiya na Abu Dhabi ya karrama shi da lambar yabo ta Gwarzon Wanzar Da Zaman Lafiya a Afirka “Award for Strengthening Peace in Africa”, ya ce akwai bukatar a samar da dabi’u da bin ka’idoji na hakuri da zaman lafiya a cibiyoyin ilimi, musamman a tsakanin matasa.
Ya bukaci shugabanni da su ba da fifiko kan ci gaban matasa, tare da taka tsantsan da ra’ayoyin da za a iya aiwatar da su wajen inganta sana’o’i, tare da magance zaman kashe wando.
Shugaban ya ce zaman banza ga matasa da rashin sanya hannu wajen tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu da kuma makomarsu na nuni da alhakin da ke tattare da nahiyar musamman a bangaren tsattsaurara ra’ayi ga masu tsattsauran ra’ayin.
Shugaba Buhari, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar, ya ce dole ne a hada karfi da karfe wajen dakile yaduwar kananan makamai da kuma hana yaduwar manyan makamai a nahiyar Afirka.
Shugaban ya yi kira kan muhimman batutuwan taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka na gaba da su yi nazari mai zurfi kan kalubalen da ke ci gaba da kunno kai a kasar Libya tare da fatan samar da ingantacciyar hanyar da Afirka za ta warware matsalar rashin zaman lafiya da aka kwashe shekaru 10 ana fama a kasar ta Libya da a yanzu ta zama mafaka ga kowane nau’in makamai da mayaka na kasashen waje wadanda babban tasirinsu ke fuskantar yankunan Afirka ke fama da shi.
“ Shugabanni, Mambobi masu girma, mata da maza, ku sani ta’addancin duniya, ‘yan fashi da sauran laifuffukan kasa da kasa na ci gaba da haifar da manyan kalubale ba ga Afirka kadai ba, har ma ga zaman lafiya da tsaro a duniya. Wadannan al’amuran sun zama barazana na dindindin ga ci gaban tattalin arziki da ci gaban al’umma.
“Nijeriya da sauran hukumomin shiyya-shiyya a Afirka da ma sauran kasashen duniya suna aiki tukuru domin tunkararwa kan wadannan barazanar da ke tattare da wanzuwar bil’adama. A garemu a Nijeriya, muna ci gaba da yin hadin gwiwa tare da bangarori daban-daban don samun galaba a kan yaki da ‘ yan ta’addar Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci da ke da alaka da su.
“Lokacin da na karbi mulki a 2015, Boko Haram sun rike kusan kashi biyu bisa uku na Jihar Borno, rabin Jihar Yobe, da kuma wasu kananan hukumomi biyu a Jihar Adamawa, duk a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Mun samu damar dawo da wadannan yankuna ta hanyar zuba jarin sama da Dala biliyan 1 don samun makamai masu linzami daga Amurka da sauran kasashen kawayenmu don gudanar da ayyukan ci gaba da yaki da ta’addanci tun daga 2015.
A nasa jawabin, Shugaban Dandalin Wanzar da Zaman Lafiya a Tsakanin Al’ummar Musulmi, Shaykh Abdallah Bin Bayyah, ya bayyana taken taron na 2023 cewa dogara ne da shawarwarin “Sanarwar Nouakchott” da ke da nufin rushe tushen addini na maganganun masu tsattsauran ra’ayi da kuma takaita tashin hankali bisa dalilai na addini da aka sanya a matsayin takardar bayani a cikin ra’ayin zaman lafiya na Afirka a taron kolin shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka karo na 33.
Da yake maraba da shugabanni da masana na Afirka wajen taron zaman lafiya, shugaban kasar Mauritaniya ya ce an ba shugaba Buhari lambar yabon ne saboda samar da shugabanci nagari da kuma samar da zaman lafiya a kasa mai kabilu da al’adu da harsuna da dama kamar Nijeriya, tare da kara gogewa da hikimarsa zuwa sauran kasashen Afirka.