Hukumar Shige Da Fice ta Nijeriya (NIS) ta samu gudunmawar na’urorin aiki na miliyoyin nairori daga Kamfanin IHS da ya yi shuhura a duniya wajen samar da kayan aiki na sadarwar zamani.
Kamfanin ya bai wa NIS na’urorin ne domin Ęara tsaurara tsaro a iyakokin Ęasa musamman ganin cewa Nijeriya tana fuskantar zaÉen 2023.

Babban Shugaban kamfanin, Dakta Mohammed Darwish wanda ya damĘa gudunmawar ga Shugaban NIS, CGI Isah Jere Idris MFR, a shalkwatar hukumar da ke Abuja a yau Litinin, ya bayyana cewa kamfaninsu ya jima yana aiki kafaÉa da kafaÉa da masana’antar sadarwa a Nijeriya sama da shekara 21 da suka gabata inda ya samar da aikin yi ga sama da ‘Yan Nijeriya dubu arba’in (40,000).
Tun da farko a nashi jawabin, CGI Isah Jere ya gode wa kamfanin bisa gudunmawar da suke bayarwa ta fuskar kyautata mu’amala da zumuncin aiki, kana ya tabbatar da cewa lallai ya fara haduwa da Kamfanin ne a sama da shekara 20 da suka gabata, lokacin da yake wakiltar kujerar NIS a Majalisar BunĘasa Harkokin Zuba Jari ta Nijeriya.
CGI Isah Jere, kamar yadda sanarwar da Jami’in Sadarwa na NIS, Tony Akuneme ya fitar ga manema labarai ta ruwaito, ya yi alkawarin aiki da na’urorin kamar yadda ya dace musamman a halin yanzu da ake fuskantar zaÉe.

Kayayyakin sun haÉa da na’urorin Motorola guda 25,Ā da na sadarwa na tafe da gidanka guda 155 da sauran wasu manyan kayan sadarwa.
Daga cikin tawagar NIS da suka tarbi mahukuntan Kamfanin na IHS akwai Mataimakiyar Kwanturola Janar mai kula da sha’anin kuÉi da harkokin mulki, Misis Caroline Adepoju da muĘaddashiyar mataimakiyar Kwanturola Janar, Dora Amahin da ke kula da bincike da tsare-tsare.