Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai zaman kanta a jihar Kano a ziyarar kwanaki biyu da zai kai jihar a ranakun 30 da 31 ga watan Janairu, 2023.
Kwamishinan yada labarai na jihar kuma mai magana da yawun kwamitin gwamnan jihar Kano, Mohammad Garba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kokarin kwamitin na ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2023.
Har ila yau, Garba ya bayyana cewa, a ziyarar ta kwanaki biyu da Buhari zai kai, zai kaddamar da ayyuka da suka hada da kaddamar da cibiyar tattara bayanai da cibiyar koyon sana’o’in hannu ta Dangote da tashar jirgin ruwa ta kasa ta Dala da gidajen malamai a karamar hukumar Ungogo da tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta mai karfin Megawatts 10 da Dam din Tiga da gadar Muhammadu Bridge.
Tashar wutar lantarki ta IPP mai karfin megawatts 10 za ta samar da wutar fitilun kan titi da Masana’antu da ayyukan samar da ruwa da sauran sassa masu mahimmanci.
Da yake magana kan zaben, Garba ya bayyana kwarin gwiwar cewa dan takarar gwamna na APC zai samu gagarumin rinjaye.