Jami’ar Bayero ta Kano ta karyata wata wasikar bogi da ake yadawa a shafukan sada zumunta da ke ikirarin bayyana karin kudin shiga jami’ar.
Wata sanarwa da mataimakiyar rajistara kuma mai kula da jama’a ta makarantar, Lamara Garba ta fitar a ranar Litinin, ta ce wasikar karya ce.
Sanarwar ta ce, har yanzu mahukuntan jami’ar ba su yanke shawara kan duk wani karin kudin shiga jami’ar ba sabanin yadda wasu “masu karya ke yada wasikar karya a shafukan sada zumunta.
“Jami’ar na kira ga dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin jami’ar ba sabanin yadda wasu makaryata ke yada wasikar karya a shafukan sada zumunta,” in ji sanarwar.
Don haka jami’ar ta bukaci jama’a da su yi watsi da bayanan domin karya ce tsantsagwaronta.