Kafin zuwan ranar 31 ga watan Janairu 2023 na wa’adin da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sanar na daina karbar takardun kudi Naira 500, 200 da kuma 1,000.
Sai dai bankin ya shawarci masu ajiya a bankuna da su dinga ziyartar masu sana’ar POS, mai makon bin layin bankuna.
- Matar Aure Ta Bukaci Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta Kan Rashin Kulawa
- ‘Yansanda Sun Cafke Masu Laifi 208 Cikin Kwana 26 A Adamawa
Daraktan sashen binciken kudi na CBN, LydiaA lfa, ce ta bayar da wannan shawarar a hirarta da manema labarai a garin Yola a Jihar Adamawa.
Ta ce, ta nuna bacin ranta kan yadda mutanen da ke kin karbar tsofaffin takardun kudin tun kafin zuwan ranar 1, 2023, inda ta danganta hakan a matsayin yin zagon kasa.
Darakatar ta bayyana cewa, har zuwa yau, wadannan tsofaffin kudaden Naira 1,000,
500 da kuma Naira 200 takardu ne da jama’a za su iya karba.
Lydia ta kara da cewa, masu sana’ar POS din tamkar wakilai ne idan babu bankuna a kusa, su ma ana iya zuwa wajensu don gudanar da hada-hadar kudi.
Shi ma a nasa jawabin kwanturolan CBN na reshen Yola Sanusi Sah, ya bai wa masu ajiyar kudi a bankuna tabbacin cewar, suna da isashen lokacin da suke bukata na hada-hadar kudade.
Sanusi ya bayyana cewa, an umarci CBN da sauran bankuna da su yi aiki har a ranar Asabar da Lahadi domin biyan bukatar masu ajiyar kudade bankuna.