Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta kama mutane 208 da ake zargi daban-daban cikin kwanaki 26.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Sikiru Akande wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya kara da cewa daga cikin adadin, an gurfanar da mutum 108 a gaban kotu.
- Zanga-zanga Ta Barke A Katsina Bayan Kaddamar Da Aikin Da Buhari Ya Yi
- Mahara Sun Kashe Mutum Daya A Taron PDP A Enugu
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yansandan jihar da ke Yola, inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin yin garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma satar shanu.
Ya ce an kama mutanen ne bisa umarnin babban sufeton ‘yansanda na bukatar ‘yansanda su kara inganta aikin sintiri da dabarun kawar da miyagun laifuka.
“A farkon wannan shekarar, rundunar ta sake jadadda alkawarinta tare da tsarin tsaro don aiwatar da aikin Sufeto Janar na ‘yansanda Usman Alkali Baba.
“Tun daga watan Janairu zuwa yau, jami’an rundunar sun gudanar da sintiri na dabara da leken asiri, da kai samame maboyar miyagu tare da ayyukan.
“Wadannan ayyuka sun samar da sakamako mai kyau kuma an kama jimillar mutane 208 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu da sauran laifuffukan ta’addanci, daga cikinsu an gurfanar da mutane 108 a gaban kotu,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce bindiga kirar AK-47 guda bakwai aka kwato tare da sauran makamai.