Duk shiga maganar da Majalisar Kasa ta yi na neman Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin da ya bayar na daina karbar tsofaffin takardar kudin 1000, 500 da 200, Babban Bakin ya ce ba za a kara koda minti daya ba a wa’adin da aka sanya na ranar 31 ga watan Janairu 2023. Hakan ya sa ‘yan Nijeriya cikin dimuwa.
Al’umma a sassan Nijeriya na ci gaba nuna fargabar su a kan karancin sabbin kudin da aka sauya wa fasali a tsakanin al’umma da kuma kalubalen da suke fuskanta a ya yin da suke kokarin mayar da tsofaffin kudaden su Banki.
- Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamna Ya Rasu A Adamawa
- An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 5.6 A Gundumar Luding Ta Lardin Sichuan Na Kasar Sin
Wannan kuma ya sanya masu gudanar da harkokin kasuwanci da dama sun fara dari-dari wajen karbar tsofaffin kudaden ya yin da a wasu sun fara kin karbar kudaden gaba daya.
Kudaden da suka hadsa da takardar Naira 1000, 500 da 200 duk kuma da Babban Bankin Nijeriya na CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairu ne a matsayin ranar da za a dakatar da karbar tsofaffin kudin, sai kuma gashi sabbin kudaden basu yalwatu ba a cikin al’umma.
Rahotattnin da Waklilanmu na sassan kasar nan suka tattaro mana ya nuna cewa, al’umma na cikin dimuwa da fargaba, ana kuma ganin ana iya shiga rudu a fannin rayuwa da tattalin arziki a Nijeriya in har ba a samar da mafita ba ga wannan matsalar.
sun bayyana cewa, CBN ya samar da sabbin kudin ne na Naira Biliyan 200 kuma abin da ake bukata ya kai fiye da Naira Tiriliyan 3.1 abin da ya sa masana ke ganin shi ne babban dalilin halin da ake ciki na karancin sabbin kudaden.
Bayani yan nuna cewa, a haln yanzu masu harkar canjin kudin su mayar da harkar canjin kasuwanci inda ake saye da sayar da sabbin a unguwar zone 4 da ke babba birnin tayarra Abuja ya zama dandalin sayar da sabbin kudaden.
Talaka A Kano Ya Shiga Tsaka Mai Wuya
Yayin da ya rage ‘yan kwanaki wa’adin da Babban Bankin Kasa CBN ya gindayawa duk wani mai tsoffin kudi ke kare a ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2023, ko shakka babu talaka a Jihar Kano kamar sauran jihohi na fuskantar mummunar barazanar tafka asara, ganin yadda kusan aka kwashe rabin wadancan kwanakin da babban Bankin Kasa ya tsara wadatar da al’ummar kasa da dabbin kudade. Kasancewar suma.
A Jihar Kano tun ranar 21 ga watan da muke ciki wasu manyan ‘yan Kasuwa suka shelanta daina karbar tsoffin kudade, ya yinda daukacin wuraren fitar da kudi a (ATM) na Bankuna ke ci gaba da biyan Jama’a da tsoffin kudade.
Wata babbar Matsalar ma itace yadda masu POS suka shiga rufe wuraren kasuwanci su, kasancewar cikin mutum goma da za su shiga wurin su domin mu’amalar kudi, zakatarar tara daga cikin kwastomin kawo kudi suke bukatar a saka masu asusun bankunan su, haka suma masu shagunan sayar da kayan masarufi a wasu unguwannin da Jaridar Leadership Hausa ta zaga, ta fahimci Jama’a da yawa sun zabi rufe shagunansu, kasancewar suna cikin tsaka mai wuya.
Na farko duk wanda zaizo sayayya da tsoffin kudi zaizo, can kuma manyan diloli dake Kasuwar Sabon gari da Singa na barazanar cewa daga lokaci kaza ba za su karbi tsoffin kudade ba. Su kansu masu Baburan adai-daita Sahu sun shelanta ranar da za su aje baburansu domin gujewa karbar tsoffin kudade.
A Kasuwannin kauye kuwa irin Kasuwar Tudun Wada inda ake safarar shinkafa da dangogin amfanin Gona, Manoma da dillalai kowa ya rike
amfanin gonarsa sun dakatar da kawowa kasuwanni gudun kar suyi cikin kifi a ruwa, su sayar da kayansu a basu tsoffin kudade, ya yinda su ana su bangaren ma akwai Kananan Hukumomin da a Jihar Kano babu Bankin Baki daya ga Kuma masu POS sun hakura.
Yanzu haka layukan dake Bankuna a Kano na Neman zarta layin man fetur tsawo, ya yinda talakawa kowa ya yi tagumi, leburori Suma rana zafi, inuwa kuna, sai ka fita sannan a samo abin sawa a bakin salati, ka tashi daga leburanci a biya ka da tsohon kudi, kazo sayayyar abinda za’a kaiwa iyali domin sarrafawa mai kanti ko mai awo ya kekasa kasa cewa shi ba zai karbi tsohon kudi ba.
Abin da ake fata shi ne ganin yadda sabon matakin da babban Bankin Kasa ya fito dashi na zaga dukkan kananan Hukumomin kasarnan Baki daya, inda aka tsara karbar tsoffin kudade bisa wani adadi ko dankuwa mutum bashi asusu ajiya an tsara na ta kw za’a bude Masa asusun ajiya a saka masu kudin aciki. Wannna na nuninda cewa Bankin na Kasa bashida niyya tsawaita lokacin daina mu’amala da tsoffin kudaden.
Ana Turuwa Zuwa Bankuna A Kebbi
Wasu kwastomomi a Birnin Kebbi, wadanda suka yi tururuwa zuwa bankuna domin yin ajiya ko karban kudade, sun kuma nuna matukar damuwarsu kan karancin samun sabbin takardun Naira.
Duba da Bankunan da ke Birnin Kebbi da Wakilin LEADERSHIP Hausa ya gano cewa kwastomominsu da yawan gaske sun yi cincirindo a bankuna daban-daban suna kokarin shiga bankunan ko kuma samun su cire kudi a Automated Teller Machines (ATM).
Da yake magana a wata tattaunawa da wakilin Leadership Hausa a bakin bankin UBA a Birnin Kebbi, Malam Musa Gero daga Kukaru, Gulma a karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi, ya ce tun karfe 6:00 na safe ya ke kan layi. Amma duk da hakan bai samu damar shiga bankin ba.
“Na yi sama da sa’o’i biyar ina nan ina jiran layi in ajiye kudi na, kamar yadda nake magana da ku ni ne mai lamba na 260 saboda jami’an bankin sun rubuta sunayenmu kuma sun ba mu lamba, don haka har yanzu muna jiran layi ya kawo gare ni. ” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba halin da ‘yan Nijeriya suke ciki a jahohinsu ta kuma tsawaita wa’adin zuwa wani lokaci domin daukar duk wani abu, idan ba haka ba mutane da yawa za su kirga asara tun kafin karewar wa’adin.
Malam Musa Gero ya tuna cewa ya kasance mai mutukar son shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin ya zama shugaban kasa, “amma ga dukkan alamu manufofinsa sun sabawa bukatun talakawan Nijeriya, inji shi.
Shima a wata zantawa hira da aka yi da Malam Muktar Sambo a harabar First Banki, daga kauyen Zogirma da ke karamar hukumar Bunza, ya koka da cewa a fadin yankin ba su da ko banki ko daya da za su iya yin ciniki.
Ya ce: “Muna tafiya tun daga Bunza domin mu zo nan mu ajiye kudadenmu tunda ba mu da banki inda za mu shiga mu ajiye kudinmu.
“Lokacin ya yi kadan saboda sun ce 31 ga wata za a rufe karbar tsofaffin takardun Naira, saboda hakan mun zo nan ne mu ciro Naira dubu 100,000 amma sun ce mutum zai ciro iya addadin Naira dubu 40,000 ne kawai a na’urar ATM ba bayar wa.
“Wani irin mugunta ne wannan, wanda ke da kudinsa ba zai iya ciro Naira dubu 100,000 kamar yadda babban bankin ya gindaya, muna rokon gwamnati ta janye matakin da ta dauka ta hanyar tsawaita wa’adin don baiwa ‘yan Nijeriya damar cin gajiyar arzikin da suke dashi.”
A nasa bangaren, Malam Ibrahim Hassan, daga karamar hukumar Birnin Kebbi, ya ce tun karfe 7:00 na safe ya ke kan layi na Guaranty Trust Bank (GTB). Ya ajiye kudinsa domin cimma wa’adin ranar 31 ga watan Janairu.
“Ina daya daga cikin wadanda suka fara zuwa banki domin ajiye kudi, ina nan kafin karfe 7:00 na safe amma babban abin mamaki shi ne har yanzu ina da mutane sama da 100 a gabana a kan layi,” inji shi. .
Ibrahim Hassan ya koka kan rashin samun sabbin takardun Naira da basu yawo a jihar, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake duba manufofinta ko kuma ta kara wa’adin.
“Ko a banki a yanzu idan kana son cire kudi har yanzu suna ba ka tsofaffin takardun kudin Naira, wannan shi ne ya shaida maka cewa ko bankin a akwai karancin sabbin takardun Naira.
Wakilinmu ya kuma lura cewa idan aka yi la’akari da lokaci da karancin sabbin kudade da ake fama da su tun daga ranar da aka tsara, 15 ga Disamba, 2022 don fitar da sabbin takardun kudin Naira da dama, mutane da yawa ba za su iya cika wa’adin 31 ga watan Janairu ba.
Jama’a Na Cikin Fargaba A Jihar Kogi
Duk da tsarin da Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya bullo da shi na bin mutanen karkara, wato mazauna kauyuka domin karbar tsoffin kudaden dake hannayensu, yana musanya musu da sabbi, gabanin karewar wa’adin da bankin ya bayar,wato 31 ga watan Janairun 2023, na dakatar da amfani da tsoffin kudaden, wato naira 200 da 500 da kuma 1000, jama’a duk da haka,sai kokawa suke ci gaba da yi na ganin babban bankin na Nijeriya ya tsawaita wa’adin saboda gudun kada yan kasuwa sun tafka asara duk da cewa wasu sun yaba da tsarin da babban ya bullo dashi na sauya fasalin kudaden da kuma hana amsar tsoffin kudaden tun daga ranan 31 ga watan janairun 2023.
Wakilin Jaridar LEADERSHIP Hausa a Jihar Kogi, wanda ya tattauna da jama’a, musamman yan kasuwa dake birnin Lakwaja, ya ruwaito cewa duk da wannan matakai da babban bankin CBN ya dauka, hakan bai hana mutane tafiyar da al’amuransu na yau da kullum ba.
Ibrahim Lawal, wani dan kasuwa ne, dan asalin karamar hukumar Mani ta Jihar Katsina, wanda ke sana’ar sayar da magungun gargajiya na addinin musulunci (Islamic traditional Medicines) a tsohuwar Kasuwar Lakwaja.
Ya shaida wa wakilimmu cewa kawo yanzu su yan kasuwa, suna da babban matsala, musamman a bankunan da suke kokarin turo tsoffin kudaden don musanya musu da sabbi, yana mai kokawa da cewa wannan matsala zata fi shafar mazauna karkara wadanda akasarinsu basu da cikakken labarin sauya fasalin kudaden da wa’adin da babban bankin na CBN ya bayar, lamarin daya bayyana da cewa hakan zai jefa al’umma da dama cikin asara da talauci.
“Ibrahim ya ce, Ina da mutane abokan harkokin kasuwancimmu wadanda suke zaune a kauyuka, wani daga cikinsu ya kira mu, wai yana so ya kawo kudinsa a canja masa ganin cewa a yanzu a Katsina inda yake, an dakatar da karbar tsoffin kudaden, amma mu a nan Kogi, ba a dakatar tukuna ba, amma a gaskiya, akwai mutanenmu dake fuskantar matsoli na canja kudaden, musamman mutanemmu dake yankunan karkara, kamar yadda nayi maka bayani a baya, saboda lokaci ya kure.
” Toh, akwai wanda ya turo mana kudadensu daga can Jihar Katsina, ya nemi a taimaka a canja masa, mun kai masa bankin, amma bamu samu damar cire masa kudaden ba,saboda haka muka shaida masa cewa ya yi hakuri, sai abubuwa sun daidaita nan gaba.
Shi kuma a nasa bangaren, wani dan kasuwa dake garin Lakwaja, Muhammed Bako, maraba lale da manufofin babban bankin na CBN ya yi, inda ya ce hakan zai harzika yan kasuwa su tashi haikan wajen ganin sun inganta sha’anin harkokinsu na kasuwanci, duk da cewa ya zargi yan siyasa da manajojin bankunan da yin zagon kasa da sabon tsarin, yana mai cewa bullo da sauya fasalin kudaden yana da matukar muhimmanci, amma yan siyasa suna kokarin hada baki da manajojin bankuna domin ganin sun sanya kafar ungulu a tsarin, lamarin da a cewarsa zai jefa miliyoyin yan Nijeriya cikin halin yani yasu.
“Idan ka lura, yan siyasa suna baiwa manajojin bankunan makuden kudade don basu sabbin kudaden saboda burinsu na siyasa, kenan, talaka ne zai wahala”.
Bako, har ila yau ya dorawa ‘yan Nijeriya laifi game da lamarin.
“Idan bera nada sata, toh, daddawa ma nada wari, domin idan zaka lura, babban bankin Nijeriya ya fito da wannan tsarin na sauya fasalin kudaden kusan watanni biyu ke nan, amma wasu yan Nijeriyan sun nuna halin ko in kula. Da yawanmu muna harkar kudade, amma muka rika ajiye tsoffin kudade a shagunanmu, wasunmu ma basa kaiwa bankuna duk da cewa suna da asusun bankin. Kaga ka tara makuden kudade a banki, maimakon kaje ka ajiye a asusun bankinka, sai ka ajiye a gida ko shagonka, sai daga baya ka riga kokarin kaiwa bayan ka san lokaci yana kurewa a sakamakon wa’adin da babban bankin na CBN ya bayar.
“Kamar ni, kowani kwanaki biyu nake kai kudadena banki na ajiye, saboda irin wannan rana.
“Wasu suna gani kamar manufofin gwamnati bata aiki, kuma manufofin ta yi aiki idan bukatar hakan ta taso, kamar yadda muke gani a yanzu.
Sai dai ya ce babban matalar da ake fuskanta a yanzu wanda kuma shi ne cikas, shi ne rashin wayar da kawunan jama’a musamman na yankunan karkara ta hanyar amfani da gidajen radiyo da sauran hanyoyin sadarwa kamar shela ko gangami.
A karshe, ya kawo shawarar ganin bankuna sun shiga yankunan karkara domin budewa mazauna yankunan asusun ajiyar banki domin samun saukin lamarin.
Al’ummar Kananan hukumomi 6 Marasa Bankuna sun cikin tsaka Mai wuya a Zamfara
Sakamakon wa’adin amsar tsafin kudi ya kusa cika yanzu haka, Kananan hukumomi 6, wadanda suka jada da Bakura, Bukuyum, Maru, Tsafe, Birni Magaji da Zurmi, suna cikin tsaka mewuya a yanku nan su sakamakon rashin inda za su kai tsafin kudadan su day za’a amsa. kuma masu POS suna sun yanke Shawara kin amsar tsafin kudin daga Litinin da ta gabata harzuwa cikar wa’adin.
LEADERSHIP HAUSA, ta nemajin ra’ayin Umar Hassan Tsafe ya bayyana mana cewa, tun ranar Lahadi nake Gusau, bankin UBA ,sun amshe mani tsafin kudin kuba Babu sababin dan haka bansan yadda zanyi na koma gidaba.inji Umar Tsafe”
Ya kuma kara da cewa, yanzu haka Abu mani waya cewa, mata masu kananan sana’oi suma sun daina amsar tsafin kudin gashi kuma sabbin basu wadata ba a birni balle akauye.dan hak nake kira ga wadanda alhakin wannan canza kudi ya ke akan su da su taimama a kara wa’adin amsar tsafin kudin kuma su wadatar da bankuna ta yadda talaka ba zai sha wuya ba.
Wani da ya fito daga Bukuyum da ya nemi asakaya sunan sa ya bayyana ma Wakilin mu cewa, masu daukar Mutane dan neman amsar kudin fansa suma yanzu sabin kudi suke yi nema abasu ga wanda suka sace ko su kashe shi haka suke cema ‘yan uwan mutanan da suka Kama.
A yankin Kauran Namoda kuwa, suma mutanen Zurmi na cikin mawuyacin halin duk da matsar tsaro dama ta sanya babu ba Bankuna.suma Kauran Namoda suke zuwa domin nan ke da bankuna.dan samu canza kudin.
A Gusau kuwa babban birnin Jihar Zamfara, Bankuna cike suke da Mutane wajan amsar kudin kuma a POS kuma mutane kwana suke bin layi akarshe kuma kudin suka kare batare da sun samu ba.
Kuma yanzu haka Kananan’ ‘yan Kasuwa sun daina amasar tsafin kudin, kuma gashi a kasuwannin Basu wadata ba jama’a na cikin tsaka mai wuya
- Barazana Ce Ga Tattalin Arzikin Jihohin Borno Da Yobe
Al’ummar jihohin Borno da Yobe sun koka dangane da yadda wa’adin canja tsoffin takardun kudin da Babban Bankin Nijeriya ya kakaba, al’amarin da suka ce yana yiwa tattalin arzikin su mummunan barazanar karyewa, sun kara da cewa, hakan ya na zuwa ne sakamakon kin tura isassun sabbin kudaden a bankuna a lokacin da wa’adin yake gabatowa.
Jama’a da dama a yankin sun bayyana fargabar abubuwan da canjin kudin zai iya jawowa ba. Sun nuna matakin canja tsoffin kudin a matsayin wanda ba a yi tunani ba kafin aiwatar dashi, musamman ta hanyar kin la’akari da jihohin Borno da Yobe ba, wadanda suka sha fama da kalubalen tsaro, wanda hakan ya jawo tufe rassan bankuna da dama a jihohin.
“Idan za a iya tunawa, jihar Borno ta na da kananan hukumomi 27, kuma kafin matsalar tsaron, akwai rassan bankuna a mafi yawan kananan hukumomin; amma yanzu kananan hukumomi hudu ne kacal ake ba bankuna a fadin jihar Borno- su ne Maiduguri, Jere, Biu da Kwaya-kusur. A jihar Yobe kuma, daga cikin kananan hukumomi 17, hudu ne kawai suke da rassan bankuna; Damaturu, Potiskum, Gashu’a da Nguru.”
LEADERSHIP ta zanta da jama’a kan wannan batun, ya yin da Shugaban kungiyar yan kasuwa a karamar hukumar Potiskum, kuma cibiyar Kasuwanci a jihar Yobe, Alhaji Nasiru Mato ya ce, “Wannan mataki ya yi tsauri sosai ga talaka, inda harkoki suka tsaya cak- saboda yadda babu sabbin kudin kuma wasu yan kasuwa sun dakatar da karbar tsoffin kudin, don kaucewa asara.”
“Sannan a yanayin jihar Yobe, shi ne muna fuskantar karancin bankuna kuma ba a kawo sabbin kudin ba, ka ga kenan hakan zai shafi tattalin arzikin mu. Kuma mafi yawan al’ummar mu mazauna kauyuka ne, idan manomi ko talaka ya na kawo kayan gona ko dabbarsa domin ya sayar ya yi cefane ne kawai, kuma ba kowa ne yake da asusun banki ba a kauye. Kuma ina bankunan suke a nan Yobe?”
“Bisa ga kiyasin da muka yi, kowane mako ana hada-hadar kasuwancin sama da naira biliyan biyu a garin Potiskum; saboda yadda muke da manyan kasuwanni; kasuwr dabbobi da ta kayan abinci. Wadanda kuma ake zuwa ci daga kusan kowane bangarorin kasar nan da wasu kasashen waje. Muna da manyan motocin dakon kaya kusan suna zuwa kowane lungu da sakon kasar na. Kuma ga wannan halin da aka jefa mu na canjin kudi, wanda ba a yi tunani ba kafin a aiwatar dashi ba.” In ji shi.
Shima da yake tofa albarkacin bakin shi, Shugaban kungiyar yan kasuwar jihar Yobe, Alhaji Usman Mu’azu, ya bayyana fatan su ga gwamnatin Tarayya wajen duba halin da jama’a suke ciki tare da rokon kara lokacin, inda ya ce, “A makonnin da suka gabata, jami’an Babban Bankin Nijeriya (CBN) dake nan Damaturu sun tara mu domin fadakar damu kan matakin canjin tsoffin kudin, wanda daga bisani muka sanar da shugabanin yan kasuwa a kananan hukumomi.”
“Sannan mun bukaci su taimaka mana wajen kara lokacin wa’adin canja tsoffin kudin, amma sun nuna muna abu ne mai kamar wuya.”
a ce sakamakon mawuyacin halin da ake ciki, harkokin kasuwanci sun yi kasa sosai, kuma hakan zai shafi tattalin arziki da jihar Yobe baki daya.
Wani dan kasuwa a birnin Maiduguri, Alhaji Usman Abubakar, ya ce, “Wa’adin canjin tsoffin kudin ya daurewa mutane kai, musamman mu yan kasuwa; shin idan ka dena karbar tsoffin kudin to dame za ka gudanar da kasuwancin, saboda sabbin kudin basu wadata ba. Saboda ni din nan da nake magana da kai yanzu, a matsayina na dan kasuwa, sau biyu ko sau uku na taba ganin sabuwar dubu daya, amma da idona ban taba ganin sabuwar naira 500 ba, balle kuma 200. Saboda haka mu wannan al’amarin ya daure muna kai, abin nan fa za a yi haihuwar guzuma; da kwance uwa kwance. Da talakwa da suke zuwa sayen kayan da mu yan kasuwar da ita gwamnatin kanta duk wannan hasarar za ta shafemu.”
“Sannan kuma, ko dai gwamnati ta daga wannan wa’adin ko kuma ta koma jami’an gwamnati su zauna su nutsu domin sake nazartar yadda tsarin zai yuwu, ko kuma ta shafi kowa.”
A nashi ra’ayin, Dr. Babayo Liman, a zantawarsa da yan Jarida a birnin Maiduguri, ya ce, “Ya kamata gwamnati ta kalli wannan al’amarin da idon basira tare da sauraron korafin talakawa, a matsayin su na yan kasa kuma da la’akari da lokacin dimukuradiyya ake ba a lokacin mulkin soja ba. Sannan a baya ma an yi irin wannan canjin kuma iyayenmu sun sha wahala, kuma mafi yawan al’ummar mu mazauna kauyuka ne, kuma sabbin kudin bai wadata a hannun bankuna ba.” In ji shi.
Ya haifar Da Komawa Baya A Huldar Kasuwanci A Neja
Ranar Littinin din makon nan huldar jama’a da bankuna cikin garin minna da wasu sassan jihar Neja samun koma baya, musamman ganin yadda ta’ammulin kudade ya samu tsaiko na rashin yalwartuwar kudaden a bankuna.
Malam Aliyu Mai Leda, ya ce maganar gaskiya wannan wa’adin akwai bukatar duba shi domin yanzu haka ina da tsbbacin tsoron da ke cikin zukatan mutane sakamakon rashin amsar tsoffin kudaden daga wasu yan kasuwa.
Da yawan manyan yan kasuwan mu ba su ba mu kaya, domin sabbin kudaden ba su yalwatu a hannun jama’a ba, kuma idan ma karba tsarin adadin kudaden da bankuna za su bayar ga kwastomomin su a gaskiya ya yi kadan, idan ka tafi canji a bankuna kamar wata bakar kasuwa ce aka bude masu, domin duk dubu dari idan za a canja ma sai ka biya ma ta dubu uku.
Malam Aliyu ya cigaba da cewar maganar cashlest kuma ai kasar ba ta yi wannan zurfin ba, saboda yawaitar barayin yanar gizo kuma tsaro, maganar gaskiya idan an kawo wannan tsarin dan gyara ne ko zamanantar da tsarin mu’amalar kudi gaskiya an tafka kuskure babba.
Wani bawan Allah da LEADERSHIP Hausa ta zanta da shi a daya daga cikin bankuna lokacin da yake kan layin karbar kudi a akwatin ATM, ya ce jiya Lahadi na zo su ba ni naira dubu hamsin kai tsaye na’urar taki, bayan na samu dubu asirin sai da na tafi neman rancen dubu asirin wajen wani dan sayen kayan gyarar mota ta, lokacin da na zo yin transfer ma wancan din kudin ya fita daga asusun ajiya ta amma bai shiga wancan ba, kuma bai dawo ba.
Takaicin hakan yasa na shiga bankin dan yin korafi aka ce wai na wuce iyakar abinda aka ce in cira ne a wuni kudin bai dawo ba sai wajen goma
na dare, to ka ga wannan abin akwai cutarwa, ya kamata ne idan ma ba ka iya cire adadin abinda ka ke bukata ga mai ilimi da wayau a ba shi damar yin transfer dan cigaba da bukatun shi.
Ba wa’adin ba, tsarin ma gaba daya bai yi ba. Duk wani bankin da ka sani a cikin garin minna idan ka je za ka tarar da costomer ran shi a bace,
to da ke gari ke ya mutanen karkara za su kasance, gaskiya ya kamata gwamnati da babban bankin Nijeriya su yi kyakkyawar nazari kan wannan halin da jama’a ke ciki a sauya fasalin wannan tsarin.
Baba Ali Tadakura, wani matashi ne da ya bayyana ma wakilin mu cewar, sanya wannan wa’adin akwai bukatar dubawa dan yin gyara, domin zai shafi lamurran kananan kasuwanci, yanzu masu POS da ke zuwa kasuwannin kauye an ba su dama ne na yin yadda suka so da kudaden mutane.
Akwai manyan garuruwa a jihar nan, kamar Agaie da Katcha kananan hukumomi ne tsoffi amma saboda rashin hanyoyi bankuna sun bar wuraren, dubban jama’ar da ke zaune a wadannan kananan hukumomin dole sai sun yi tafiyar awa hudu zuwa biyar kafin shiga Minna ko Bida sannan za su iya batar da kudaden hannayensu.
Ni dai na gamsu da canja fasalin kudin saboda dalilan tsaro da kuma ruf da cikin da ake zargin wasu da yi da ya jefa kasar a wannan halin, amma
akwai bukarar ayi kyakkyawar nazari a kan sauran talakar kasar nan. Domin maganar gaskiya in har wa’adin na nan akan 31 ga watan Disambar shekarar za a jefa mutane da dama cikin mummunar hali.
Al’ummar Bauchi Da Gombe Na Cikin Zullumi
Al’umma a jihohin Bauchi da Gombe sun shiga cikin zullumi sakamakon sauyin fasalin kudi da kuma karatowar wa’adin daina amfani da tsoffin kudade da babban bankin kasa (CBN) ya bayar, lamarin da ya sanya al’umma da dama fargabar amsar tsoffin kudade.
A binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa sabbin kudade sun yi matukar karanci a fadin jihar Bauchi da Gombe, yayin da wasu da dama ma ba su taba ganin sabon kudin da idonsu ba.
A ta bakin wani dan kasuwa, Adamu Dahiru da muka tattauna da shi, “Ni ban san ma ta yaya zan saba da sabon kudin ba domin ana ta ce mana wasu za su iya fitar da kudin na bogi su yada cikin al’umma. Don haka ni gaskiya na fi son a sayi kayana a ba ni tsohon kudin nan. Mu dai muna fatan a kara mana lokaci domin mu gano inda aka dosa da yadda za mu gane sabon kudin na hakika don gudun cutar da mu. Kuma babbar matsalar ma shine ni dai ba na ganin ana hada-hada da takardar sabon kudin nan sosai.”
Shi kuwa, Alhaji Muhammadu Aminu daga jihar Gombe, ya bayyana cewar, “Yanzu in ka shiga banki ka fara jira har sai ka ji kamar ka yi yaya, mutane suna kokarinsu na zuwa domin shigar da tsoffin kudade amma gaskiya akwai karancin hanzari da cinkoso. Sannan kuma abun damuwar shine ba a baiwa mutane wadatattun sabbin kudade idan suka je bankuna neman kudi.”
Sannan wata mata mai suna Halima Ayuba a jihar Gombe ta yi kira ga CBN da ta kara tsawaita lokacin daina amfani da tsoffin kudade tare da yin kiran a kara wayar da kan al’umma musamman na karkara domin kauce wa janyo wa jama’a da dama asara.
Da LEADERSHIP Hausa ta tuntubi wani dillalin kudi na POS a jihar Bauchi, Sulaiman Alhassan, ya shaida cewar babu wadatattun sabbin kudaden nan a hannun jama’a, ya kara da cewa har zuwa ranar Talata da muke zanta da shi da tsoffin kudaden nan suke amfani.
“Ka san wani babban abun damuwa a wannan lamarin shi ne yadda jama’a basu yarda ko gamsuwa kai tsaye da ka basu takardar sabon kudi. Akwai wasu nau’in mutane da sun zo wajena ba ma fara dauko musu sabon kudin domin za su ki karba ko su yi ta wasi-wasi. Sannan, da a ce sabbin kudaden sun wadatu sosai a cikin al’umma to da sauki.
“Amma har zuwa yanzu da nake magana da kai in ka je banki za su baka tsoffin kudade ne ba sosai suke bai wa mutane sabbi ba. Don haka akwai dai tsaiko ga lamarin.”
Ya nuna cewa, wa’adin da CBN ya bayar ba lallai ya amfani jama’a ba domin matsalolin da suke akwai a halin yanzu, “Hatta wajen na’urar cirar kudade wato ATM har yanzu ana sanya tsoffin kudaden nan. Wasu in an sanya sabbin ka ga layi sosai saboda jama’a na son sabbin,” ya shaida.
Kazalika wakilinmu ya labarto cewa yanzu jama’a da dama sun fara amfani da harkar kasuwancinsu ta wajen saye da sayarwa ta hanyar tiransifa a maimakon amsar tsoffin kudi domin kauce wa fadawa cikin karewar wa’adin CBN, “Ni gaskiya yanzu kaffa-kaffa nake yi da amsar tsoffin kudaden nan. Kawai na fi son a sayi kayana a min taransfa ta asusuna,” in ji wani dan Kasuwa, Auwal Hassan.
Masu sana’ar POS a jihar Bauchi na cigaba da nuna damuwarsu kan wahalar da suke sha, hakan ne ma ya sanya suka kara farashin kudin da suke cazan jama’a.
“Sai ka shafe tsawon awanni masu yawa idan kana son shigar da tsoffin kudade a banki,” A cewar wata mai sana’ar POS, Grace Simon.
A halin da ake ciki dai masu POS, sun canza farashin kudin da suke caja inda suka kara farashi a kan hada-hadar baya.
Wata majiya mai tushe ta bayyana mana cewa, idan mutum yana so su karbi tsohon kudi su tura masa a banki, maimakon Naira 100 a kan 10,000 da suke caji, a yanzu sai ka biya Naira 2000 a kan 10,000 idan ka zo da tsoffin takardun kudin.