Fitacciyar ‘yar siyasa kuma ‘yar gwagwarmayar kare hakkin Bil’adama, HAJIYA NAJA’ATU MUHAMMAD ta raba gari da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu tare da mara baya ga takarar PDP, Atiku Abubakar.
Ta dai bayyana raba garin ne a farkon makon nan cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar.
- An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 5.6 A Gundumar Luding Ta Lardin Sichuan Na Kasar Sin
- Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamna Ya Rasu A Adamawa
Kafar yada labarai ta DCL Hausa ta tattauna da ita, inda ta yi balbalin wasu abubuwa da ke zama kutungwilar wasu ‘yan siyasa game da zaben 2023. YUSUF SHU’AIBU ya kalli tattaunawar kuma ya rubuto wa masu karatu kamar haka:
Takamaimai wace matsaya kika dauka a siyasance?
Ka san ita siyasa idan ka shiga ba ka dainata. Domin ni ba siyasa kadai nake yi ba, ina yin gwagwarmayar yakin neman ‘yancin Bil’adama. Ita siyasa ba abu ne wanda mutum zai ce ya daina ba, amma abin da kawai na daina shi ne siyasar jam’iyya. Saboda jam’iyyunmu gaba dayansu ba su da bambancin akida, kuma jam’iyya a yadda na fahimta a yanzu a Nijeriya tun da babu akida riga ce duk lokacin da ka ga dama za ka iya sakawa, sannan kuma za ka iya cirewa ka saka wata a lokacin da kake bukata.
Misali a baya muna APP tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo ANPP daga baya ya bari ya koma CPC kuma yanzu muka dawo APC. Idan ka dauki Rabi’u Musa Kwankwaso yana PDP ya dawo APC yanzu kuma yana NNPP. Haka lamarin yake a wurin Atiku, shi ma Tinubu da a AD yake ya dawo ACN yanzu kuma yake APC, to ka ga riga ce.
Amma wane ne mutumin da yake sanye da wannan rigar? Shi ne abin da al’umma ya kamata su duba. Ni yanzu abin da na yi shi ne, na yarda rigar APC, amma ina siyasa. Shi ya sa na dauki wanda na fi yarda da shi a cikin ‘yan takarar. Misali, na dauki Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa ba na Tinubu, na dauki Binani a APC a matsayin ‘yar takarar gwamna a Jihar Adamawa, sannan na dauki Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) na jam’iyyar NNPP a matsayin dan takarar gwamna a Jihar Kano, to idan na ce zan zauna a cikin jam’iyya ka ga zan iya cin amanar jam’iyya. Tun da ba na son cin amanar jam’iyya kuma babu wanda yake bina bashi, dole a halin da kasarmu take ciki idan har muka ce za mu bi jam’iyya mun yi hauka, dole sai dai mu bi dan takara, saboda haka ne nake bin mutum ba jam’iyya ba.
Idan muka kalli Tinubu, a kwanakin baya an ga hotonki tare da shi kuma ma har ya baki mukami a cikin kwamitin yakin neman zabensa, me ya sa kika ajiye wannan mukamin har kika fice daga APC da yake takara?
Wato abin da ya faru, tun farkon farawa da Tinubu ya shigo APC ni ban goyi bayansa ba, saboda ni ban goyi bayan a yi mulki irin na kama-kama ba. Amma shi Tinubu da ya tsaya takara ya ce dalilin tsayawarsa takara shi ne yanzu lokacinsa ne, shi ne zai yi shugaban kasa. Saboda haka kasa ta zama ta kama-maka ta wane da wane, idan wani ya gama, sai ya bai wa wani ya ci wanda ‘yan kasa ba su da zabi kuma ba a ba su zabi ba. Idan ma a ce so suke su bai wa Bayarbe me ya sa ba a bai wa Osibanjo ba?
Abin da ya sa na fice daga tafiyar Tinubu da APC shi ne, ya kira ni tun daga farko bayan ya lashe zaben fitar da gwani, sai ya kira ni lokacin da zai fitar da kwamitin yakin neman zabe. Inda wani yaronsa ya kirana wanda ban ma san sunansa ba sai daga baya, mai suna Falake ya ce, za a ba ni daraktan hulda da kungiyoyin fararen hula, nan take nake masa ba na so. Ya ce me ya sa ba za ki yi ba, na ce masa Tinubu bai fada min dalilin da ya sa yake takara ba da kuma abin da zai yi wa arewa.
Sai ya ce don Allah in yi hakuri na karba domin idan na zauna da Tinubu har ya fada min maganar da ban gamsu da ita ba sai in bari, sai na ce masa to. Washagari, Tinubu ya kira ni a waya da dare, ya ce min yana Ingila ya ji an ce na ki amsar mukaminsa, na ce masa kwarai domin ba ka fada min abin da za ka yi wa arewa ba. Sai ya ce don Allah in zo in same shi a Ingila. Washagari na nufi Ingila, muka zauna da shi har na tsawon awanni biyu. Amma a wannan awanni biyun, tambayan farko da na yi masa ita ce, me za ka yi wa arewa? Me ka tanadar mana? Sai ya ce min babu komi bai tanadi komi ba. Na ce ba ka tanadi komi ba, kana nufin ka ce za ka yi takarar shugaban kasa amma ba ka da wani tsari da za ka yi wa al’umma, ya ce bai yi ba. Na ce me ya sa? Ya ce ba zai yi wani tsari ba sai ya ci zabe, sai na ce a ina aka taba yin haka? domin idan ka ci zabe za a karkatan maka da hankali, yanzu ne ya kamata ka fada wa al’umma abubuwan da ka yi musu.
Ya ce min idan har ina da abin da nake so a yi wa arewa, in je in kawo masa. Na ce shi kenan muna da tawaga kuma wane shi ne shugabanmu, zan same shi.
Na ce na sami wanda yake shugabancin tawagarmu, na zauna da shi. Cikin mako guda muka fito da tsare-tsare na bukatun arewa da suka hada da harkar Almajiranmu, harkar ilimin ‘ya’yanmu, harkar aikin gonan, musamman harkar tsaro, na aje kundin domin in kawo masa tun ina Landan, lokacin da na yi waya da wanda yake min iso da shi kan cewa kundin nan da aka ce in kawo na tattara na kawo kuma ina son ganin Tinubu domin in mika masa. Sai ya ce min yanzu sai dai in yi hakuri, saboda Gwamna Nasiru el-Ruba’i ya kawo bukatar arewa na samar da ‘yansandan jihohi kuma har rana irin ta yau ban sake zama da Tinubu ba, ba su amshi bukatunmu na arewa ba, kuma ba a ce za a yi wa arewa komi ba.
Hajiya me ya sa kika nuna goyon bayanki ga Atiku Abubakar?
Na bi shi ne saboda na san suna da kyakkyawan tsari kan harkar tsaro, suna da tsari wanda aka nuna min a zahirance kan maganar da ta shafi matasanmu kan zaman banza da sauran ire-iren wadannan. Amma shi Tinubu abin da ya sa na bar shi kenan saboda ya ce bai da tsari ga arewa.
A baya-bayan nan wanda ba a yi mako guda ba, akwai wani gidan radiyo da na saurari na ji Tinubu yana fadin cewa ya fito da tsari wanda ya ayyana tsaro, samar da ilimi da bunkasa tattalin arziki, ba ki samu kin ga wannan kundin nasa ba ne?
Abin da nake kokarin fada maka shi ne, ba kundi yake da shi ba, cewa ya yi yana da ajanda, amma bai ce yana da tsari ba. Yana da ajanda a manufofinsa, dole sai ka kididdige yadda za ka yi aiki, ga yadda zan gyara harkokin ‘yansanda, ga yadda zan gyara soja. Amma ka ce za ka gyara soja to ta ya ya.
Hajiya kin fita daga cikin jam’iyyar APC bayan kin san sirrin yakin neman zaben Tinubu, wani zai iya cewa me ya sa sai da kika gama sanin sirrin jam’iyyar kika ajiye tafiyar Tinubu kika rungumi tafiyar Atiku?
Ai babu wani sirri a cikin APC, mene ne sirrin? Ka taba jin sirri a cikin harkar siyasa? Abu da ake na jam’iyya babu wani sirri a ciki. Kwaba kawai suke yi a wurin yakin neman zabe. Tun da aka saka ni darakta ba a taba kira na wata ganawa ba, ba a bata gayyata ta wurin gangami ba, babu abin da ya shahafe su.
Me ya sa ba ki dauki wani mataki ba tun a baya sai da ya rage saura kasa da kwanaki 40 kafin zabe?
Abin da ya sa shi ne, na yi ta kokarin bin hanyoyi da yawa ta yadda za a yi a gyara, kuma abin da yake kara damu na a kullum idan Tinubu ya fita ina ganin yadda yake, domin ba wai laifinsa ba ne saboda shi ciwo Allah ne yake dora wa bawansa, shi tsufa kuma rahama ce, amma akwai ka’idojin da mu Musulmi Allah ya dora mana kan maganan limanci ko shugabanci. Wanda kullum ina ganin cewa Tinubu ba zai iya ba ko ina so ko ba a so kuma komin iya karyar mutum. Kullum ina kara fahimtar cewa ba sa so ire-irenmu mu dinga ganewa, amma mun riga mun gane tun da dole zai fita gudanar da harkokin kamfe. An wayi gari sai a ce “kar ka yi magana, kawai idan ka je ka ce mun gode, sai a saka kida a yi rawa.”
Abin da nake fada shi ne, tun farko abin da ya sa ma na yi, rokona ya dinga yi da sunan Allah, da ban hakuri, ni kuma ba na so na nuna girman kai, amma tun farko sai da na ce musu ba zan yi ba, suka dinga roko na don Allah don Annabi, kuma tun da aka ce don Allah don Annabi ba zan ce ba zan yi ba. Lokacin da na gane tafiyar ta saba wa dokar Allah kuma idan har na ci gaba da zama, zan zalunci al’umma kasa gaba ki daya. Abin da (‘yan siyasar) suke so kawai Tinubu ya yi shugabanci domin ya danne musu kan maciji su yi ta wasa da bindi.
Ba ki ganin cewa Tinubu ya zo da tsare-tsare tare da kawo matasa masu jini a jika?
Wani tsare-tsare, mutum ko magana bai iya ba, kuma mai ya sa za mu ci gaba da yi wa kanmu karya? Idan a kan Buhari mun yi kuskure ba mu sani ba, wannan Allah ya nuna mana gaskiya karara, kuma muna rokon Allah kan cewa kasarmu ta shiga cikin wani hali. A zancen nan da nake maka ana kashe wasu, an sake wasu, ana yi wa mata fyade, miliyoyi mutane ba su da abin da za su ci, sai mu dinga wasa da rayukan mutane.
Amma shi Tinubu yana da laifi a kan wannan abin da ake yi?
Yana da shi, domin ya san ba zai iya ba amma ya ce yanzu lokacinsa ne, ba cewa ya yi saboda halin da Nijeriya ta shiga ya gyara ba, sai ya ce lokacinsa ne.
Kina magana a kan cewa akwai zarge-zarge kan Bola Ahmad Tinubu, amma kuma a cikin makon nan muke ganin cewa har Festus Keyamo ya lashi takobin sai ya kai Atiku Abubakar kotu saboda zargin almundahana?
To ya kai shi, amma shi kansa Festus Keyamo babu sharrin da bai yi wa Buhari ba, kuma yau shi yake wa Buhari aiki. Abin da nake cewa ba za a yi badakala da ni ba kuma ba za a yi karya da ni ba, domin ban dogara da kowa ba sai Ugangijina. Ina kokarin in fitar da gaskiya iya fahimtar da Allah ya ba ni, ba zan yi komi ba domin in samu komi, saboda ban da bukatar komi a wurin kowa sai Ubangijina. Ba da ni za a yi wannan karya ba su je su yi tayin abinsu.
Wasu na ganin watakila kamar kina ganin ko da Bola Tinubu ya ci zabe ba za ki sami mukami ba ne ko wani abu ba ne haka shi ya sa kika bar tafiyar?
A’a kai kake fadar haka, to ai dama ni ba ni da bukatar wani mukami. Yanzu ce maka aka yi Atiku zai ba ni mukami?
To wata yarjejeniya kuka yi da Atiku Abubakar?
A’a, wannan ba abin da ya shafeka. Amma ce maka aka yi na je wurin Atiku ne domin yarjejeniya, ni ba na yarjejeniya kafin na goyi bayan dan takara.
Akwai ‘yan takara manya guda hudu amma kika zabi Atiku Abubakar. Idan ‘yan Nijeriya suka tambaye ki mene ne ya sa kika zabi Atiku Abubakar?
Maganar da nake fada maka shi ne, na zauna da Atiku Abubakar, kuma abin da na nema a wurin Tinubu shi na nema a wurin Atiku Abubakar. Kuma an ba ni, na kuma gamsu, saboda suna da manufofi ba cewa suka yi suna da ajanda ba. Suna da kundi kan yadda za a yi da maganar ‘yansanda, da yadda za a gyara harkokin noma, da abin da za a yi wa matasa komai a kiddige, wanda Tinuba ya ce bai da shi.
To amma wani zai ce a 2019 Atiku ya fito takara me ya sa ba ki goya masa baya ba a wancan lokaci sai yanzu?
Saboda bai nemi in goya masa baya ba, kuma a lokacin bai zaunar da ni ya ce min ga abin da yake so ba, bai neme ni ba. Da ya neme ni, ina tabbatar maka da cewar wallahi da ban yi Buhari ba. Kuma ina son ka gane cewa akwai mutanenmu da yawa da suke cewa su ba za ma su kara kada kuri’a ba, saboda su ba su yarda da kowa ba. Maganar ita ce, ba za ka yanke kauna ga Allah ba, domin ba zai yiwuwa. Ni a matsayita ta musulma ba zan taba yanke kauna ga Allah ba, sannan ba zai yiwuwa kuma kullum kwanan duniya muna rokon Allah ya ba mu mafita, sai Allah ya rubuta mana gaskiya a zahiri, sai mu ce ba mu yarda ba mu ki bi. Ni ba haka nake ba, ba zai yiwu ba muna rokon Allah ya ba mu mafita kuma ku zauna a gida mu ki yin zabe.
Ba ki ganin wani zai ce anya kin auna wannan zabin naki sosai kuwa?
Kowa yana da ‘yancin yin zabinsa. Ni na yi nawa zabin kuma kowa zabi ya rage gare shi, ni kuma babu wanda ya isa in yi abu domin shi, ya kamata ku gane haka.
Ya kamata ka gane duk tambayan da za ka yi ka gane ni a kan akidata, saboda ni ba na abu domin mutum. Saboda mutum bai isa ya yi mun komi ba, saboda haka ni na yi zabina, zabi ya rage na sauran mutane.
Abin da wasu suke ganin cewa Atiku Abubakar yana fuskantar matsala a cikin gidansa kan wadannan gwamnoni guda biyar anya wannan zai haifar masa da da mai ido?
To sai me? Babu inda babu munafukai, domin ko a gidanka akwai munafukai, kuma don kana da munafukai tare da kai ba zai zama cewar ka fasa tafiya ba, dole ka ci gaba da harkarka.
To amma akwai alamar nasara kenan?
Da karfin Allah.
Mene ne sakonki na karshe ga ‘yan Nijeriya da suke ta dakon dama su ji kin fito kin yi karin haske kan ficewarki daga jam’iyyar APC?
Ai ni na riga na fadi dalilaina. Na yi ne a kan akida, na yi ne a kan cewa ba a da ajanda kuma lokaci ya kure, ba mu da lokacin da za mu tsaya muna ta shirme, domin saura kwana nawa zabe? wa yake da lokacin shirme yanzu. Lokaci ne da za mu wayar wa juna kai kuma abin da nake kokari kenan.