A halin da ake ciki kuma, Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC ya mayar da martani kan bayanan Naja’atu kan watsi da dan takararsu na shugaban kasa Bola Tinubu, inda kwamitin ya ce Naja’atu Mohammed cikin banci ce a wurinsu wanda hakan ya sa suka kore ta.
Ya ce Naja’atu ta kasance tsohuwar daraktar hulda da kungiyoyin fararen hula a cikin kwamitin yakin neman zaben APC, amma saboda rashin kwarewa da fadace-fadace ne ya sa suka kore ta.
- Kaso Mai Tsoka Na Ra’ayoyin Jama’a Ya Nuna Gamsuwa Da Nasarar Kasar Sin A Fannin Kandagarkin COVID-19
- Karancin Man Fetur Da Sauya Kudade Shiri Ne Na Hana Zaben 2023 —Tinubu
A ranar 19 ga watan Janairun 2023, Naja’atu ta mika wasikar ajiye aiki ga shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu, inda ta bayyana cewa ta ajiye mukaminta sakamakon matsalolin da Nijeriya ke fuskanta tana bukatar ci gaba da fafutukar samun ingantacciyar kasa.
Amma a cikin wata sanarwa da mashawarci kan harkokin da suka shafi jama’a na yakin neman zaben APC, Mahmud Jega ya fitar, ya ce Naja’atu tana yaudarar ‘yan Nijeriya cewa ita da kanta ta ajiye aiki bayan kuma korar ta aka yi daga kwamitin yakin neman zaben na APC.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, Jega ya ce, “Tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu/Shettima ba ta samu takardar Naja’atu Mohammed na ajiye mukaminta a matsayin daraktar hulda da kungiyoyin fararen hula ba kafin a kore ta sakamakon rashin kwarewa da fadace-fadace, bayan ta yi watsi da gargadinmu na bai wa abokan adawa bayanan sirri.
“Duk da ta kasance tana yaudarar ‘yan Nijeriya da cewa ita da kanta ta ajiye mukamin, wasikar korarta tana nan kan teburinta a ofishinta. Ta kasance cikon banci, tun lokacin da aka kore ta daga yakin neman zabe, take ta sambatu.
“Ta kasance ‘yar siyasa mara akida da take takama da kwarewa kuma ba ta da ita, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC yana mamakin yadda Naja’atu wacce ta kasance ba likita ba amma take shakkun lafiyar Tinubu bayan likitoci sun tabbatar da cewa zai iya yin mulkin Nijeriya.
“Ko kungiyar likitoci za su kori magananta bisa zantar da hukuncin kan lafiya ba tare da yin gwaji ba.
“Duk da shi ne dan takarar shugaban kasa a 2023 da ya fi sauran ganin nasara a bayyana, amma Tinubu ya ziyarci mafi yawancin sassan kasar nan domin yin gaggamin yakin neman zabe da ganawa da kwararru da al’ummomi da kungiyoyin ‘yan kasuwa da kungiyoyin addinai,” in ji Jega.
Ya kara da cewa maganar da Naja’atu take yi cewa lokacin da ta tambayi Tinubu shirin da ya yi wa ‘yan arewa, sai ya ce bai da shi, wannan zance kawai ne.
“Tinubu yana da kyakkyawan tsari kan kasar nan, musamman matsalolin da suka shafi arewa. Lokacin da Tinubu ya halarci taron gamayyar kungiyoyin arewa a shekarar da ta gabata, ya bayyana musu irin abubuwan da ya tanada wa arewa.
“Muna kira ga magoya bayanmu a dukkan kasar nan su yi watsi da duk wata suka ga tafiyar Tinubu/Shettima ga ‘yan siyasa mara ka’ida.”