ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karancin Man Fetur Da Sauya Kudade Shiri Ne Na Hana Zaben 2023 —Tinubu

by Sadiq
4 years ago
Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana matsalar karancin man fetur da kuma shirin sauya fasalin kudi da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bullo da shi a matsayin wani shiri na kawo tsaiko ga zabe mai zuwa.

Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su bari karancin man fetur ya sanyaya musu guiwa kan gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

  • Ministan Harkokin Wajen Argentina: Sin Muhimmiyar Abokiyar Cinikayya Ce Ta Argentina
  • Xi Jinping Ya Gabatar Da Sakon Bidiyo Ga Taron Koli Karo Na 7 Na Kungiyar Kasashen Latin Amurka Da Caribbean

Tinubu ya bayyana karara cewa karancin man fetur da ake fama da shi tamkar zagon kasa ne sannan ya danganta lamarin da cewar da gangan na haddasa shi.

ADVERTISEMENT

Dan takarar na APC ya bayyana haka ne a Abeokuta, yayin yakin neman zabensa a Jihar Ogun.

Yayin zargin cewar an hada baki da yin barna wajen samar da wutar lantarki, inda ya danganta sauya fasalin kudade da aka yi a matsayin wani shiri na dagula wa mutane lissafi.

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

“Ko sun ce babu mai a kasa, za mu yi tattaki don kada kuri’a. Sum yi barna da yawa don haka za su iya cewa, babu mai. Wannan zai iya haifar da rikici ta hanyar zagon kasa ga wadatar mai a kasa.

“Suna yin zagon kasa ga samar da mai. Ko man fetur ko babu za mu je mu kada kuri’a kuma za mu yi nasara. Wannan juyin juya hali ne mafi girma kuma idan na fada muku, kun san abin da nake nufi. Kun san ni ne zan sauya komai.

“Sun yi ta shirin haifar da matsalar mai, amma a manta da komai. Ni, Asiwaju zan magance matsalar samar da mai har abada.

“Ni dan gida ne, na zo nan, kuma ba zan ba ku kunya ba, za mu karbi mulki.

“Wannan juyin juya hali ne, wannan zabe juyin juya hali ne. Sun yin makirci, amma za su sha kasa. Sun ce farashin mai zai karu kuma zai kai Naira 200 kowace lita.Ba sa son a gudanar da wannan zabe, suna son a murde shi,” in ji Tinubu.

Da yake magana game da tsare-tsarensa ga matasan Nijeriya, Tinubu ya yi alkawarin bullo da shirin ba da lamuni ga dalibai, tare da samar da tsarin ilimi wanda zai magance matsalolin malamai da tabbatar da cewa dalibai sun kammala karatu a lokacin da ya dace.

“Ina ba ku tabbacin abu daya: zan bai wa dalibai lamuni. Babu wanda zai daina zuwa Jami’ar saboda kudin makaranta. Ina ba ku tabbacin cewa babu wanda zai sake maimaita shekaru ba tare da ya kammala karatunsa ba.”

MASU ALAKA

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa
Manyan Labarai

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
An Kama Tsohon Minista Uche Nnaji Kan Zargin Amfani Da Takardun Bogi
Da ɗumi-ɗuminsa

An Kama Tsohon Minista Uche Nnaji Kan Zargin Amfani Da Takardun Bogi

July 1, 2026
Next Post
Qin Gang Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Ma’aikatar Harkokin Wajen Gabon Bisa Rasuwar Ministan Harkokin Wajen Kasar Michael Moussa-Adamo

Qin Gang Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya Ga Ma'aikatar Harkokin Wajen Gabon Bisa Rasuwar Ministan Harkokin Wajen Kasar Michael Moussa-Adamo

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.