Shafin da ke zakulo muku batutuwa da suka shafi al’umma, ta fanni daban-daban, kama daga fannin Zamantakewa na rayuwar yau da kullum, Zaman Aure, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da matsalar da wasu matan ke fuskanta na dukan da mazajensu ke yi musu, wanda kuma sanadiyyar hakan ke haifar da matsaloli da dama ga ma’auratan, ta wani fannin ma har da yaransu.
- Daga 2016 Zuwa 2020, An Kashe Dala Biliyan 6 Wajen Shigo Da Alkama -CBN
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da matsalar da wasu matan ke fuskanta na dukan da mazajensu ke yi musu, wanda kuma sanadiyyar hakan ke haifar da matsaloli da dama ga ma’auratan, ta wani fannin ma har da yaransu.
Dalilin hakan shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa, inda suka bayyana nasu ra’ayoyin game da wannan batu; Ko mene ne amfanin dukan Mace a zamantakewar aure?, Zaman Aure da duka ya halatta ne ko kuwa?, Ko me hakan zai iya haifarwa a zamantakewar auren?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Aminu Idris Abdulwahab Ikara LGA, Jihar Kaduna:
Sam! dukan Mace ba shi da wani amfani a zamantakewar Aure, facema kawo cikas da nakasu da yakewa Auren. Hakan bai halatta ba, domin dukan mace a zamantakewar Aure ba halin kirki bane. Dukan mace a zamantakewar Aure kan dakusar da dukkanin wata soyayya da farin cikin dake cikin Aure daga karshe har ta kai ga rugujewar Auren gaba daya. shawarata ga dukkanin masu Dukan Matansu shi ne; su tuna cewar hakan babban kuskurene da kuma rashin sanin darajar Auren kanshi, domin duk wanda ya san darajar Aure ba zai taba iya dukan matarsa ba.
Sunana Abba daga Zamfara:
A gaskiya ba shi da wani amfani, don yana kawo raini a tsakananin ma’aurantan, amman abin da yake sa ayi dukan 3 ne; wani daman halinsa ne, wani kuma maybe yana shaye-shaye, wani kuma gaskiya kure shi aka yi, ba shi da wata mafita dole sai yayi dukan, sanan zai iya hucewa don maganar gaskiya duk macan da ka ga an doka to ita ce ta sayi dukan da kudinta. Amman ai kowa ya san bai halarta ba, kawai dai tana kama wani har an yi dukan. Shawara daya ce a rinka sawa zuciya hankuri a daina biye musu don mace sai da hankuri.
Sunana Princess Fatimah Mazadu:
Gaskiya duka ko a musulunce abu ne mai muni, bai da amfani kwata-kwata, kawai na fi daukar duka a zamantakewar aure da ganganci ko raini daga wajen mijin, watakila akwai dalilin da ya sa ya ke dukan nata wani. Bai halattaba, amma ya halatta ta wani wuri da manzon Allah (s.a.w) ya ce; “kakan iya kama gefen bakin rigarka ka dake ta in a misalce ranka yayi mugun baci kololooo”. Yama jaho Mugun raini, rashin zaman lafiya, rashin ganin mutuncin juna, gashi dai kamar duka ya zamo ruwan dare a wannan zamanin, abu kadan namiji ya ce zai daki mace, ko ma ya zage ya nada mata duka kamar jaka, Allah ya kyauta, matanku abun tattali amma wasu abun wofi da banzatarwa suka maida su. Mummanan duka bai halatta ba a aure, wasu ni ina mamakinsu wallahi, ba su ciyar da matansu da kyau ba sai duka, wasu kuma shaye-shaye ke janyo hakan. Mata anan ina kira a garesu su rage gautsi da masifa da neman fada, dan yanzu maza elbow suka iya ba tattaliba, saboda haka mata ‘yen uwana mu kiyaye sai a samu zaman lafiya. Bangarem maza ina kira a gare su da su daina dukan mata, saboda yawan duka kan iya nakasa mutum, ko ya kai ka ga aikin dana sani, dan wani dukan na kashe bawa, wani na raunata wa, a sanyaya zuciya zama ne na hakuri, zo mu zauna zo mu saba watarana, amma in an yi hakuri sai aci nasara. Allah ya shiryamu baki daya. Albarkar manzon Allah, maza su daure suke koyi da halin manzon Allah gadon hakuri da kauda kai (s.a.w).
Sunana Abba Ismail daga Jihar Kano:
Gaskiya dukan mace a zaman takewar aure bai dace ba kuma babu kyau duk da dai addini ya tanadar da yadda za ka yi a muslunci idan karantse, sabida duk namijin dake dukan matarsa tamkar yana yi wa kansa tabo ne na har abada wanda ba zai taba gogewa ba, kuma ‘ya’yansu ma ba za su dinga ganin girmansa ba, jama’ar gari ma ba za su dinga mutunta shi ba. Dukan mace babu kyau gaskiya, sai dai kuma indai kuma ka riga ka rantse kamar yadda muslunci ya tanada sai ka kama bakin rigarka ka dan daketa ta hana rantsuwa rigar ma wacce ba za ta cutar da ita ba sabida ka rantse. Haifar da rashin mutuntata juna da rashin jituwa da rashin dorewar auran ma baki daya. Shawara shi ne; su roki ubangiji yayi musu su daina shi ne za su rayu cikin farin ciki da walwala.
Sunana Fatima Jaafar Abbas Rimin Gado LGA Jihar Kano:
Gaskiya babu wani amfani game da dukan mace a zamantakewar Aure, Saboda mace tanada rauni bai kamata a dinga dukanta ba, saboda rayuwar aure an ginata ne akan nutsuwa, soyayya, da rahma a tsakanin ma’aurata. Idan haka ne to miji yayi watsi da wannan baya Jin tausayin matarshi ko kadan. Gidan fatawa na misra sun ce; “Dukan mace ko zaginta Asharin ‘HARAMUNNE’, wanda ya aikata ya aikata zunubi ne, saboda babu wata Aya a Alkur’ani ko Hadith daya nuna haka. Duka zai iya haifar da rashin jituwa tsakanin Maauratan guda biyu, har ya kai ga an yi abin da Allah baya so wato ‘SAKI’ Shawarar da zan ba su shi ne; Miji ya ji tsoron Allah ya daina dukan matarsa, su kuma tuna kalar gudummawar da matansu suke basu su dinga tausaya musu, kuma suma Mata su dinga kiyayewa.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Dukan mace ba shi da wani amfani, duk da a cikin alkur’ani an ambaci dukan sai dai ba irin dukan da ake yi musu bane a yanzu. Bai halatta ba, kai tsaye sai an biyo matakan shari’a. Hakan zai haifar da rashin mutunta juna, rashin ganin kimar uban daga ‘ya’yansu, saboda suna gani ana dukan mahaifiyarsu, sannan duka baya kawo gyaran hali. Shawara su ji tsoron Allah su daina, don hakan rashin tausayi ne da wulakanci gami da zubar da kima da mutunci, sai kuma matan su rinka kiyaye dokokin mazajensu don a zauna lafiya.
Sunana Amina Mu’awuya Mukhtar:
Dukan mace a zamantakewar aure ba shi da wani amfani. Zaman aure da duka bai hallata ba kwata-kwata. Babu abin da dukan mace ke haifarwa a zaman aure face raini, kaskanci, sannan za ta daina ganin abokin zamannata a matsayin miji, idan da ‘ya’ya a tsakani kuma za su raina shi, sannan su dinga ganinsa a matsayin mugu mara tausayi. Ita ma fa wacce kake duka abar so da kauna ce ga iyayenta da kuma danginta, amma suka dauka suka baka ita a matsayin abokiyar rayuwa, wacce za ku tallafi juna ku kuma rufawa juna asiri. Ta bar iyaye, dangi ta zabi ta zauna da kai, da kuma danginka ba tare da ta saba da su ba, toh kai maye ribarka idan ka doketa. Ita ma fa mutum ce tamkar kai ‘ya’yanku ba za su taba mantawa ba. Kuma kai ma idan aka yi wa ‘yarka abin da kake yi wa ‘yar wani ba dadi za ka ji ba. Ko dabba ma idan aka doke ta sai Allah ya saka mata balle Dan Adam me daraja.
Sunana Auwalu Abdullahi Umar Kiru, Jihar Kano:
Aure wani abu ne da duk wani addini da al’ada suka yarda ayi tsakanin mace da namiji, wacce ta haka za a samu zuriya hallattacce a kowanne sako da lungu na duniya. Musamman, a addininmu na musulunci sunna ce mai karfi idan Allah (SWA) ya baka iko da ka rayata gwargwadon iko. Duka a zamantakewa ta yau da kullun bai dace ba, ballantana ma a babbar zamantakewa mai albarka kamar ta Aura. Babu wani amfani da hakan zai kawowa ma’aurata, danginsu, iyali da sauran al’umma face nadama da kuma danasani. Bugu da kari kuma a addininmu ma abu ne wanda bai da gurbi baki daya. Zaman Aure bai halatta ba kwata-kwata domin dukan ba irin wanda malamai suka yi magana akansa ba ne. Irin dukan da ake yi musamman wanda miji yake yi wa matarsa bai dace ba. Duka a zamantakewar Aure zai haifar da wasu abubuwa kamar haka; Fushin uban giji, Gushewar so, Tsangwama, Raini, Rashin fahimta ko matsaloli tsakanin iyaye, Rabuwar kai tsakanin iyali, tamkar ana koyar da yara wannan mugunyar dabi’a/halayya. Rugujewar Aure da dai sauransu. Shawarwari ga maza masu irin wannan halayyar ya kamata su dauka sun hada da; Biyayya ga dokokin Allah (SWA), Samin ilmin abin(Aure) kafin ayi shi. Kai zuciya nesa, kara hukuri akan kananan abubuwa, Nazari mai zurfi, Rashin magana ko mayar da martani idan rai ya baci, Tausayawa da mutunta mata, Saka magabata a ciki don neman mafita idan abun ya ci tura da dai sauransu.