Wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne, sun raba wa matafiya kyautar tsofaffin kudi masu yawan gaske a Jihar Borno.
An rawaito cewa, sun yi rabon kudaden ne a kauyen Mairari daura da babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno da ke a karamar hukumar Guzamala.
- Tsohon Shugaban Jam’iar Bayero Ta Kano, Farfesa Ibrahim Umar Ya Rasu
- NIS Ta Samar Da Fasfo Kimanin Miliyan 2 A Shekarar 2022 —Gwamnatin Tarayya
An ruwaito cewa, mayakan ISWAP na sanye da kakin soji dauke da kudi mai tarin yawa.
A cewar wani mazaunin yankin, Bakura Ibrahim, ‘yan ta’addar sun tsaya ne a kasan wata bishiya suka kuma ja dunga a kan hanyar dauke da wasu jakankuna shake da tsofaffin kudaden, inda ya kara da cewa, mun taso daga Monguno da misalin karfe 12 na rana a cikin motarsu kirar Golf Volkswagen suka tunkari kauyen Mariri.
Ibrahim ya ce mayakan sun dakatar da su sannan suka tambaye su ko Maiduguri za su je, wanda nan take suka raba musu dubu 100 kowanensu.
Shi ma wani da ba a bayyana sunansa ba ya ce, “‘Sun ce mana sun ba mu kyauta muje mu je bankuna mu canja su zuwa sabbin kudi.”