Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, ta dauki matakin kawo karshen yadda ake samun fasa gidajen yari a sassan kasar nan, inda daurarru kan gudu. Fasa gidan yari na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a watan Satumba 2022 a Kuje, Abuja, inda daurarru ciki har da rikakkun masu manyan laifuka suka tsere bayan da ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan yarin.
A martaninsa, shugaban kasa ya gaggauta amincewa da a samar gidajen yari na zamani masu dauke da cikakken tsaro guda shida a sassan jihohin kasar nan, ciki har da wanda ake ginawa a garrin Karshi da ke a kan iyakar Jihar Nasarawa da yankin babbar birnin tarayya Abuja wanda ake sa ran zai iya daukar akalla mutum 3,000 a lokaci daya.
Sabon gidan yarin da za a gina da sauran da za a gina a wasu sassan Nijeriya an shirya samar da kudaden ginawa ne ta wasu kudade daga asusu na musamman da Shugaba Buhari ya amince da su, hakan kuma na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na sake fasalin gidajen yarin ta yadda za su yi daidai da zamani, ana son su tashi daga yadda aka san su a da na wajen gallaza wa mutane zuwa gidan gyaran hali.
Sabon gidan yarin da ake ginawa a garin Karshi zai iya daukar mutum 3,000 maza da mata zai kuma samar wa da ma’aikatan hukumar gidajen yari ofishoshin gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba.
Shirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsayu don samar da kudaden yi, ana kuma sa ran kammalawa a cikin watan Mayu na wanannan shekarar, ana kuma sa ran shugaba Buhari ne da kansa zai jagoranci bikin kaddamarwa kafin wa’adin mulkinsa ya kare a 29 ga Mayun wannan shekarar.
Samar da sabon gidan yarin na daya daga cikin matakai masu muhimmanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka don sake fasalin gidajen yarin kasar nan wanda hakan ya sa tun da farko aka sanya mashi suna daga Gidaje Yarin Nijeriya zuwa Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya.
Amma wani abin dubawa anan shi ne inda aka shirya gina daya daga cikin gidajen yarin, wato garin Karshi.
Rahottanin sun nuna cewa, akwai wajen fasa duwatsu a tsakiyar inda ake gina gidan yarin, a kan haka ne nuna damuwa a kan abin da fashe-fashen da za a rinka yi zai iya haifarwa ga irin wannan gidan na ajiye manya da kananann masu laifi ga abin da zai iya haifarwa ga lamarin da ya shafi tsaro da jami’an tsaron gaba daya. Wani kamfanin fasa dutse sun bayyana cewa, wajen nasu ne da suka mallaka ta hanu ma’aikatar albarkatun kasa, kuma sun mallaki filin ne da izinin gwamnatin tarayya, kuma suna aiki ne kamar yadda doka ta tanadar.
Tun da farko, Hukumar Babbar Birinin Tarayya ta musammaya musu da wani filin ga Hukumar gidaje amma sai aka yi haka a bisa kuskure daga baya kuma aka fahimci kamfanin fasa duwatsun yana aki ne a karkashin dokokin Nijeriya na ‘Land Use Act of 1978, Sections 44 (3)’ na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 sashi na 1 na dokokin Albarkatun Kasa na Nijeriya na shekarar 2007.
A bisa dubi ga muhimmancin tsaro na kasa, kamfanin fasa duwatsun ya shirya barwa hukumar gidajen yarin wajen tare da komawa wani wajen daban amma suna neman lallai a biya su diyyar asarar harkokin kasuwanci da za su yi sakamakon asarra harkokin kasuwan ci da za su yi in har sun tashi daga inda aka san su.
Masu ruwa da tsaki a harkokin hakar ma’adanai sun sanya baki inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta biya kamfanin fasa duwatsun diyyar asarar da za su yi sakamakoin mamaye wurin da hukumar Gidajen Yarin ta yi.
A ra’ayin wannan jaridar, duk da shirin gwamnatin Buhari na samar da gidajen yari na zamani da zai ka ga kawo karshen matsalolin da ake fuskanta a harkokin gudanar da gidajen yari a Nijeriya, yana kuma da matukar muhimmanci a warware dambarwar da ke tattare da kamfanin fasa duwatsu na Karshi don samar da fahimtar juna da kuma kawo karshen rashin jituwar da ake fuskanta don a tabbatar da yi wa kowa adalci.
Haka kuma lallai shirin samar da gidan yari na zamani wani hangen nesa ne mai matukar muhimmanci, mussamman ganin yin haka zai karfafa yadda ake gudanar da harkokin gidajen yarin kasar nan, amma kuma yana da matukar muhimmanci a tabbatar da yin haka bai cutar da wani ba a cikin masu ruwa da tsaki ciki har da kamfann fasa dutse da ake takaddama da shi a halin yanzu a yankjin Karshi.
Kamfann fasa dutsen, kamfani ne na zamani yana kuma dauke da kayan aiki na zamani, ana kiyasta cewa, shi ne na uku a fadin tarayyar kasar nan, masu zuba jari ‘yan kasa da abokan kasuwancinsu na kasashen waje ne suka kafa kamfanin tare da zuba jari na miliyoyin Nairori amma wannan dambarwar tana neman ta karya wanan kokari da wadannan masu kishin kasar suka yi.
Haka kuma ma’aikatan wannan kamfanin da a halin yanzu suka rasa ayyukansu duk ‘yan Nijeriya ne da wannnan rikicin ya sa suka rasa hanyar cin abincin su.
A matsayinmu na gidan jarida muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi a bin da ya kamata na biyan kamfanin diyyar da suka kamata tare da warware dukkan matsalolin da suka dabaibaye lamarin gaba daya a bisa lura da abin da ya shafi tsaron kasa da kuma hakki na kamfanin fasa dutsen.