Sarkin Kano mai murabus kuma Khalifan Tijaniyyah, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da ke ajiye da tsaffin kudi na naira 500 da naira 1,000 da kuma naira 200 da su yi amfani da karin wa’adin kwana goma da CBN ya yi don su kai tsaffin kudin bakunan da suke yin ajiya.
Ya ce, daga yanzu zuwa ranar 17 ga watan Fabarairu duk mai tsaffin takardun kudi ya je ya ajiye su a bankin da yake yin ajiya, wanda kuma ya yi nuni da cewa, ajiye kudin a bankin, zai taimaka wajen yin mu’amala da kudi a Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa, CBN ya bayar da tabbacin cewa, zai sa ido a kan bankunan kasar don ya tabbatar an musanya wa al’umma tsaffin kudin da sababbi.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su taimaka wajen sa ido a kan wadanda ke yin cuwa-cuwa da katunansu na ATM.
A cewarsa, akwai mutanen da ke karbar kudi daga wasu ‘yan siyasa ko masu laifi da ba za su iya zuwa bankuna da sunansu ba don su kai tsaffin kudin na su ba.
Sanusi ya shawarci ‘yan Nijeriya cewa, su kwana da sanin cewa, duk wanda ya dauki kudi masu yawa ya sa su cikin asusunsu na ajiya a bankuna, bayan kuma ana sane da cewa, kudin sun fi karfin a gansu a cikin asusunsa, EFCC na sane kuma za ta iya kiransa don ya yi bayani a ina ya samo su.
Saboda haka sai ya ce, wadanda suka tara kudi ta hanyar zalunci, shi ke nan ta kare musu, inda ya ce, wannan alhakkinmu ne ya kama su kuma bai kamata mu tausaya musu ba.