Assalaamu alaikum. Malam Allah ya kara maka imani da fahimta. Tambayata ita ce Mahaifina ne yake nuna bambanci a tsakaninmu sannan yana yawan zagin mahaifiyata musamman in kannena sun yi masa laifi sai ya kama zagin ta. Sai na nuna masa rashin jin dadi na da wannan al’amari har ya kai ga mun daga ma juna murya.
Karshe sai ya fara yi min Allah ya isa yana tsine mun, a yi mun bayani kan wannan lamari, na gode.
Wa alaikum assalam. Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin ‘ya’yansa, Annabi (SAW) yana cewa : “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin ‘ya’ya yanku”. Wannan ya sa lokacin da Sahabi Bashir ya yi wa dansa kyauta, ya nemi Annabi (SAW) ya yi shaida a kan haka, ya tambaye shi : shin duka ‘ya’yanka ka yi musu kyauta ? sai ya ce A’a, sai Manzon Allah ya ce : Ba ka so su zama daidai wajan yi maka biyayya? Ba zan yi shaida a kan zalunci ba”. Bukhari da Muslim sun rawaito wadannan riwayoyi.
Yin adalci a tsakanin iyalai yana inganta tarbiyya, yana sanyawa su ji tausayin Uba bayan ya girma, yana kara musu hadin kai da son juna.
Ya wajaba mazaje su sani cewa: zagin matayansu ya saba wa ka’idojin shari’a, kuma hanya ce ta tabarbarewar tarbiyya, domin yaran za su rabu biyu, wasu suna bayan mahaifinsu, wasu kuma Babarsu za su ga ta yi daidai.
Ya wajaba a tausasa harshe lokacin da za a yi magana da mahaifi saboda Allah ya hana fada wa Uba kalma mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya zo a Suratul Isra’i.
Ba a son ana yın muguwar addu’a ga iyalai saboda in aka dace da lokacin amsar addu’a za ta zamar masa matsala.
Allah ne mafi sani.