Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci da a zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a ranar Asabar a garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.
- Rashin Adalci Tsakanin ‘Ya’ya Yana Jawo Fitintinu (Fatawa)
- Ganau Ya Yi Karin Haske Kan Kisan Makiyaya 37 A Nasarawa
Buhari ya kara da cewa ya san Tinubu a matsayin dan Nijeriya mai kishin kasa a cikin shekaru 20 da suka gabata wanda ya ba da gudunmawa sosai ga dimokuradiyya a kasar nan.
Ya kara da cewa, an gwada Tinubu kuma an amince da shi duba da matsayin da ya rike a baya kuma zai inganta kasar nan idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Buhari ya kuma ce zai ci gaba da yi wa jam’iyyar APC yakin neman zabe, inda ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da ma mabiyansa da su zabi Tinubu a matsayin wanda zai gaje shi a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Nasarawa da su sake zabar Gwamna Abdullahi Sule a karo na biyu domin karfafa nasarorin da ya samu ta fuskar tsaro, samar da ayyukan yi, bunkasa noma da lafiya da dai sauransu.