Jam’iyyar adawa ta NNPP reshen jihar Gombe, a ranar Juma’a ta tabka babbar asara sakamakon fucewar shugaban jam’iyyar na jihar, Maikano Abdullahi, inda ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Maikano ya bayyana sauya shekar zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan wata ganawarsa da gwamnan jihar, Inuwa Yahaya.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe 2 Sun Fice Daga APC Sun Koma NNPP
- NNPP Ta Yi Mummunar Bari A Arewa Maso Gabas
Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan faru ne kasa da makonni biyu bayan da jam’iyyar NNPP ta kaddamar da yakin neman zabenta na gwamna a jihar.
LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar, Khamisu Mailantarki, ya kaddamar da yakin neman zabensa a ranar 21 ga watan Janairu a karamar hukumar Billiri ta jihar, inda tsohon shugaban jam’iyyar, Maikano, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar suka halarci babban taron suna kuma gabatar da jawabai a wurin.
Idan dai ba a manta ba a ranar 21 ga watan Janairu sakataren jam’iyyar NNPP na shiyyar Arewa-maso-Gabas, Dakta Babayo Liman, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a wani taron manema labarai da ya gabatar a yankin.