Gwamnonin jam’iyyar APC, sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a, inda suka roke shi da saka baki kan cire wa’adin daina amfani da tsofaffin kudi.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran takwarorinsa na APC ne suma gana da Buhari a fadar shugaban kasa, kan bukatar.
- Man U Ta Maye Gurbin Eriksen Da Zai Yi Jinyar Watanni Uku
- A Babban Taron Kamfanin LEADERSHIP Karo Na 14…An Zakulo Abubuwan Da Za Su Kawo Nasara Ko Cikas Ga Zaben 2023
El-Rufai ya ce sun shaida wa Buhari irin wahalar da talakawa suka shiga sakamakon tsarin takaita cire kudi da sauya tsofaffin kudi da sabbi suka haifar.
“Abun takaicin shi ne CBN sun karbi sama da tiriliyan biyu, amma iya biliyan 300 suka buga, wanda hakan ba zai isa ba.
“Mun sanar da shi irin wahalar da talakawa ke sha da kuma yadda ‘yan kasuwa ke tafka asara saboda rashin kudin da mutane za su sayi hajarsu,” in ji shi.
El-Rufai ya ce babu matsala game da tsarin canjin kudin, amma babu inda aka taba canja kudi a lokacin zabe.
Sannan gwamnan ya yi korafi game da wa’adin da CBN ya sanya na daina amfani da tsofaffin kudaden.