Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar Sa Kai 41 biyo bayan wata arangama da suka yi da ɓarayin daji a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Kakakin rundunar SB Gambo Isah ya bayyanawa manema labarai haka a Katsina acikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin yau juma’a.
A cewar sanarwar ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai da bindigogi kirar AK 47 sun yi dirar mikiya gidan wani Alhaji Muntari da ke zaune a garin Unguwar Audu Gare, Kandarawa a cikin ƙaramar hukumar Bakori inda suka kashe dabbobi 30 da shanu 50 suka shiga daji da su.
“Da samun wannan labari sai ‘yan sa kai suka shirya wata tawaga ta garuruwa 11 domin tunkarar ɓarayin daji, su kwato dabbobi da shanun da aka sata,” inji sanarwa.
A cikin rashin sa’a ‘yan sa-kai da suka bi sawun ‘yan bindiga a cikin dajin yargoje, ashe ɓarayin sun yi kwanton ɓauna nan take suka harbe ‘ysn sa kai 41 har lahira sannan suka raunata mutum biyu.
Bayan faruwar lamarin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na shiryar Malumfashi ya jagoranci zuwa inda lamarin ya afku domin ɗauko gawarwakin ‘yan Sa Kai 41 da waɗanda suka ji rauni zuwa babar asibitin Kankara
Daga karshe sanarwar ta ce yanzu haka an tura gamayyar jami’an tsaro domin kamo yan binidgar da suka yi wannan ta’asa domin su fuskanci hukunci. Kuma bincike na ci gaba da gudana.