• Leadership Hausa
Saturday, April 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ICPC Ta Cafke Ma’aikatan Banki Da Wasu Kan Boye Sabbin Kudi A Abuja Da Osun 

by Sadiq
2 months ago
in Labarai
0
ICPC Ta Cafke Ma’aikatan Banki Da Wasu Kan Boye Sabbin Kudi A Abuja Da Osun 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC), ta kama jami’an bankunan kasuwanci a Abuja da Jihar Osun bisa zargin boye sabbin kudi.

Kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya ce hukumar na ci gaba wajen dakile masu boye kudin a bankuna.

  • Canjin Kudi: Ina Sane Da Wahalar Da Mutane Ke Sha, Komai Zai Daidaita – Buhari
  • Ana Gab Da Gabatar Da Kumfyutar Quantum Na Sin Mai Suna Wukong

Wata ma’aikaciyar banki, wadda ita ce shugabar reshen bankin Stanbic IBTC da ke Deidei a Abuja, an tsare ta saboda kin saka kudi a cikin injin ATM.

A lokacin da tawagar ICPC da ke sa ido a bankin suka kai samame bankin da misalin karfe 1:30 na ranar Juma’a domin tabbatar da bin doka da oda, sun bukaci a yi bayani kan dalilin da ya sa dukkanin injinan ATM babu kudi.

Sai dai shugabar ta bayyana cewar bankin bai samu kudi daga CBN ba.

Labarai Masu Nasaba

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

Sai dai bayanan da jami’an ICPC suka samu sun nuna cewa reshen bankin ya karbi kudin ne da misalin karfe 11:58 na safe, kuma da gangan ya ki raba su ga mutane.

Wannan dai na zuwa ne bayan hadin guiwa da CBN ya yi da jami’an EFCC da ICPC don kama masu yi wa shirin canjin kudin zagon kasa.

Tuni da Babban Sufeton ‘Yansanda na Nijeriya, ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu na sayar ko boye sabbin kudin.

Tags: BankunaCBNICPCMa'aikataSabbin Kudi
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 41 A Katsina

Next Post

Amurka Ba Ta Cancanci Sukar Kasar Sin Ba

Related

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato
Labarai

9 hours ago
Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 
Labarai

Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

10 hours ago
Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami

11 hours ago
Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso
Manyan Labarai

12 hours ago
Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida
Manyan Labarai

Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida

13 hours ago
Elon Musk Ya Zarce Barack Obama Yawan Mabiya A Twitter
Manyan Labarai

Elon Musk Ya Zarce Barack Obama Yawan Mabiya A Twitter

14 hours ago
Next Post
Amurka Ba Ta Cancanci Sukar Kasar Sin Ba

Amurka Ba Ta Cancanci Sukar Kasar Sin Ba

LABARAI MASU NASABA

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

March 31, 2023
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Irin Su Na Farko A Duniya

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Irin Su Na Farko A Duniya

March 31, 2023
Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

Zababben Gwamnan Katsina Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Matsalar Tsaro Zai Fi Bai Wa Muhimmanci 

March 31, 2023
Kasar Sin Ta Bayar Da Shawarwari Dangane Da Yadda Za A Aiwatar Da Sanarwar Vienna Yadda Ya Kamata

Kasar Sin Ta Bayar Da Shawarwari Dangane Da Yadda Za A Aiwatar Da Sanarwar Vienna Yadda Ya Kamata

March 31, 2023
Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami

Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami

March 31, 2023
Ana Fatan A Hada Kai Wajen Shawo Kan Kalubalen Dake Addabar Duniya

Ana Fatan A Hada Kai Wajen Shawo Kan Kalubalen Dake Addabar Duniya

March 31, 2023
Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso

Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso

March 31, 2023
Taron Kolin Demokuradiyya Na Amurka Ya Shaidawa Duniya Ma’auni Biyu Da Amurka Ta Dauka Kan Batun Demokuradiyya

Taron Kolin Demokuradiyya Na Amurka Ya Shaidawa Duniya Ma’auni Biyu Da Amurka Ta Dauka Kan Batun Demokuradiyya

March 31, 2023
Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida

Har Yanzu Ni Ke Da Cikakken Iko A Matsayin Gwamnan Kano —Ganduje Ga Abba Gida-Gida

March 31, 2023
Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa

ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci