Kamfanin BUA ya kaddamar da aikin rubanya hanyar Kano zuwa Kazaure-Kongolam mai tsawon kilomita 132 tare da hadin guiwar ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya kaddamar da aikin na Naira biliyan 116 a wani taro a Kazaure na jihar Jigawa.
Sanarwar da BUA ya fitar ta ce, aikin zai ratsa jihohin Kano, Jigawa, da Katsina daga zagayen Dawanau a jihar Kano zuwa Kongolam a jihar Katsina.
Ministan, a cewar sanarwar ya bayyana cewa, kamfanin BUA Group ne zai dauki kashi mai yawa na daukar nauyin gudanar da aikin na rubunya hanyar mai tsawon kilomita 132 a wani bangare na ci gaba da ayyukan raya ababen more rayuwa.
Da yake jawabi a wajen taron, babban daraktan rukunin kamfanin BUA, Kabiru Rabiu, ya ce BUA zai ci gaba da jajircewa wajen hada kai da gwamnati kan muhimman ayyuka da tsare-tsare da za su hanzarta samar da ci gaban bil’adama, zamantakewa, da samar da ababen more rayuwa a fadin kasar nan.