Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta bayyana cewa mutanen jihar sun gaji da yadda jam’iyyar APC ke gudanar da ayyukanta, don haka, jam’iyyar NNPP za su kada wa kuri’unsu, duk da barazana da cin mutuncin da jam’iyya mai mulki ke yi musu.
Da yake tabbatarwa a ranar Laraba, yayin da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar Sharada, shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya yi Allah wadai da cin zarafi da muzgunawa da ake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar, ya kuma yi kira ga ‘yan sanda da su kasance masu adalci da kuma rashin nuna bangaranci acikin duk harkokin zabe mai zuwa na 2023.
“Duk da son zaman lafiyarmu, mun yanke shawarar fitowa fili mu fada wa kasa halin da siyasar jiharmu ke ciki na cin zarafin ‘ya’yan jam’iyyar adawa da jam’iyya mai mulki ke yi, kamar cin zarafi da raunata mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, musamman magoya bayan NNPP.”
A cewarsa, “Jam’iyya mai mulki na fuskantar kalubalen shan kaye a zaben. Don haka ta tsara hanyoyin da za ta bi wajen yin magudin zabe ta hanyar kai wa mambobin jam’iyyun adawa hari tare da yin amfani da ‘yan bangar siyasa da wasu jami’an ‘yan sanda marasa kishin kasa.”