A kalla mutune 16 ciki har da mambobin jami’an tsaron sa-kai na CJTF ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren da ake kyautata zaton mambobin mayakan ISWAP ne suka kaddamar a jihar Borno.
Har-ila-yau, an tattaro cewa, mayakan na ISWAP sun harbe masu sana’ar jari-bola 13 a kauyen Goni Kurmi da ke karamar hukumar Bama a jihar ranar Asabar.
Majiyoyin Jami’an tsaro sun shaida wa Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro kuma mai sharhi a kan lamuran tsaro a yankin Lake Chad cewa wadanda suka gamu da tsautsayin sun hada da maza 11 da mata 2.
Ya ce, mayakan sun zo cikin motoci hudu da kuma wasu a kan Babura inda suka mamaye yankunan tare da kaddamar da hare-haren su na ta’addanci.
Majiyoyi sun kuma kara da cewa, gomannin mutunen yankin sun arce domin tsira da rayukansu.
Kazalika, wasu mayaka dauke da muggan makamai da ake zargin ISWAP ne sun farmaki mambobin tsaron sa-kai na CJTF inda suka kashe uku daga cikinsu tare da yin garkuwa da ma’aikatan samar da agaji a karamar hukumar Monguno da ke Kudancin jihar Borno daren ranar Juma’a.
Mayakan sun yi ta barin alburusai kan mai-uwa-da-wabi daga nan suka yi garkuwa da ma’aikatan agaji 3, “sun kuma yi kokarin sace wasu motoci uku amma hakan bai yiyu musu ba. Daga nan su ka sace ma’aikatan agaji uku suka yi gaba,” cewar majiyar.
Idan za ku iya tunawa a cikin kasa da makonni hudu sama da masu sana’ar jari-bola 60 aka kashe a kauyen Modu da ke Kala-Balge da kuma karamar hukumar Dikwa a jihar.
Har zuwa lokacin fitar da wannan labarin rundunar soja ba ta fitar da wani sanarwar kan wanna harin ba.