Rundunar sojin Nijeriya ta ce akalla ‘yan ta’addar Boko Haram 204 ne da iyalansu suka mika wuya ga sojoji a jihar Borno.
Rundunar sojin, wacce ta bayyana haka a shafukanta na sada zumunta a daren ranar Laraba, ta ce ‘yan ta’addan da suka mika wuya ana ci gaba da tantance su.
- Mun Ware Sojoji 5,800 Domin Tunkarar Yaki Da ‘Yan Ta’adda —Shugaban Soji
- 12 Ga Yuni: Jami’an Soja 3 Sun Yanke Jiki Sun Fadi Yayin Gudanar Da Fareti A Abuja
Rundunar sojin ta rubuta cewa: “Harin da ake ci gaba da kai wa ‘yan ta’adda a yankin Arewa-maso-Gabas ya sake yin wani gagarumin nasara a yau, 15 ga watan Yuni, 2022.
Talla
Mayakan Boko Haram 204 da suka hada da iyalansu suka mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai a karamar hukumar Bama ta jihar Borno. ‘yan ta’addar na ci gaba da mika wuya.”
Talla