‘Yan takara uku daga cikin ‘yan takarar Gwamnan Sakkwato a inuwar jam’iyyar APC sun sa kafa sun yi fatali da zaben fitar da gwani da aka gudanar kan abin da suka kira da tafka magudi wajen tantance wakilai masu zabe, a kan hakan suka sha alwashin kalubalantar zaben.
Dakta Kabir Dasuki, jigo a Jam’iyyar APC ne ya yi wannan Jawabin ga manema labarai a madadin ‘yan takara uku da aka yi galaba a kansu, wato Ambasada Faruku Malami Yabo, Jakadan Nijeriya a Kasar Jordan da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir wanda ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa sai kuma Alhaji A.A Gumbi.
- 2023: Jm’iyyar APC Ta Fara Tantance Masu Neman Takarar Shugabancin Nijeriya
- 2023: Duk Sanatocin Bauchi Masu Ci Babu Mai Komawa Sun Sha Kaye A Mazabunsu
Ya ce ko kadan ba a bi ka’ida ba a zaben, an kuma tafka magudi don haka za su bi hakkinsu a duk inda ya kamata domin ba za su taba yadda da sabawa dokar zabe ba. Zaben da aka gudanar ba sahihi ba ne wanda kowane bangare zai iya yadda da shi ba.
“Tun daga wajen tantance deliget aka fara samun matsala, a inda za ka ga ejen din daya dan takarar, Ahmad Aliyu, da dan ubangidansa, Sanata Aliyu Wamakko a cikin mutanen da ke aikin tantance wakilai masu zabe. Kwamitin zaben da suka zo daga Abuja kawai sun zama ‘yan kallo ne kawai domin ‘yan gidan Wamakko ne suka karbe aikin tantancewar.” In ji shi.
Ya ce abin takaici ne deliget da wanda ya yi karatu da wanda bai yi karatu ba a ce duka sai dai a rubuta masu wanda za su zaba. Haka ma ya ce ana cikin zabe wutar janareta ta yi ta daukewa, aka zauna cikin duhu tare da yin abin da aka ga dama, wanda akan wadannan abubuwan ya ce za su bi hakkinsu a duk inda ya kamata.