Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya bukaci Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, ya kuma roki wakilan da za su fitar da dan takara za su zabe shi saboda ganin da suke.
Badaru wanda daya ne cikin masu zawarcin kujerar shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar APC, yanzu haka shi ne gwamnan jihar Jigawa.
Cikin wata hirar da ya yi da BBC, Gwamna Badaru ya bayyana wasu dalilin da yasa yake ganin masu zaben dan takara za su samu karfin gwuiwar zabarsa.
Talla
Cikin abubuwan da ya bayyana akwai gogewar da ya samu bayan ya shafe shekaru yana aikin gwamnati da kuma kasuwanci.
Talla