A ranar Juma’a 10, ga Febarairun 2023 wata Kotun daukaka kara ta tabbatar da Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamna a Jam’iyyar PDP a kano.
Tunda farko wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Kano.
- Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Tabbatar Da Mohammed Abacha A Matsayin Da Takarar Gwamnan PDP A Kano
- PDP A Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Sadiq Wali Da Abacha
LEADERSHIP HAUSA ta rawaito cewa alkalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin ranar Alhamis ya soke zaben fidda gwanin da ya samar da Sadik Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umartar INEC da ta maye sunansa na Mohammed Abacha.
Kotun ta amince da dukkan hujojjin wanda ya shigar da karar.
Mohammed Abacha ne ya shigar da karar yayin da wadanda ake kara su ne Sadik Aminu Wali, INEC, da kuma jam’iyyar PDP a jihar.