Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya dage taron yakin neman zaben shugaban kasa a Kano sai zuwa bayan wani lokaci.
Tun da farko dai an shirya taron ne a ranar 16 ga Fabrairu, 2023.
- Maniyyata 700 Wadanda Aka Bari A Bara Za Su Fara Tashi A Bana A Kano – Shugaban NAHCON
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Kano
Daraktan hulda da jama’a kuma mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo (SAN), ya tabbatar wa wakilinmu a ranar Juma’a cewa an dage taron.
A cikin sakon WhatsApp, Keyamo ya ce, “Eh gaskiya an dage taron.”
Da aka nemi a bayyana dalilin dage yakin zaben, Keyamo ya bayyana cewa, “Gaba daya an sauya jadawalin yakin zaben.”
An shirya taron ne a matsayin wani shiri na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima gabanin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.