A shirye-shiryen tunkarar babban zabe na 2023 mai zuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu motoci da kayan aiki na rundunar ‘yan sandan Nijeriya domin inganta dabarun aikinta.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Buhari ya yaba da kokarin Babban sufeton ‘yansanda na cika kudirin gwamnatinsa na samar da gyare-gyare na zamani, da cikakken kayan aiki, da kwazo da maida hankali ga ayyukan jami’an ‘yansanda.
Kayan aikin da aka kaddamar sun hada da motoci daban-daban guda 127.
Hakazalika, an kuma ba da wani kaso mai yawa na makamai, alburusai, da kayan kwantar da tarzoma kamar barkonon tsohuwa, riguna masu tare harsashi da sauran kayan kariya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp