A jiya Lahadi, jirgin saman dakon kayayyakin tallafin da gwamnatin kasar Sin ta samarwa kasar Turkiye, sakamakon aukuwar girgizar kasa mai tsanani a kasar sun isa filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul dake Turkiye, an kuma sauke dukannin kayayyakin tallafin a kasar.
Kayayyakin tallafin sun hada tantuna, da barguna, da sauran kayayyakin da yankunan da girgizar kasa ta shafa ke matukar bukata. Game da hakan, hukumomin da abun ya shafa a Turkiye sun bayyana cewa, za su raba kayayyakin bisa hakikanin bukatun wurare daban daban.
Haka zalika, an aike da kayayyakin tallafin jin kai da kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta samar ga yankunan dake shan fama da tasirin girgizar kasar a kasar Syria a karo na biyu daga birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, kayayyakin da ake sa ran za su taimakawa mutanen dake fama da ibtila’in sama da dubu goma.
Kafin wannan, an riga an mika kayayyakin kiwon lafiya da kungiyar ta samarwa Syria a karo na farko, hannun kungiyar Red Crescent ta kasar, domin amfani da su a yankunan da fama da ibtila’in.
Sabo da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, bayan aukuwar girgizar kasa a Turkiyya da Syria, Sin tana nuna goyon baya, da samar da gudummawa ga kasashen biyu wajen yaki da bala’in.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya yi kira da cewa, ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta soke takunkumin da aka kakabawa Syria ba tare da bata lokaci ba, da daina yin hayaniyar siyasa, alal misali sassauta takunkumin cikin gajeren lokaci. (Masu Fassarawa: Jamila Zhou, Zainab Zhang)