Abokai, kwanan baya kasar Amurka ta harbo wata balan-balan ta kasar Sin da ta yi batan hanya har ta shiga sararin samaniyar kasar ta Amurka. Kana Amurka ta shafawa kasar Sin bakin fenti ta fakewa da wannan batu, inda ta ce Sin tana haifar da barazarar leken asiri a duniya.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana gaskiyar halin da ake ciki, inda ya ce, Amurka tana amfani da kimiyya da fasaharta yadda take so a cikin dogon lokaci, don leken asirin kasashe daban-daban, ciki har da kawayenta. Kuma shigar balan-balan din Amurka sararin samaniyar sauran kasashe ba abin mamaki ba ne.
A shekarar bara, balan-balan din Amurka sun ratsa sararin samaniyar kasar Sin fiye da sau 10 ba tare da samun izninin Sin ba. Idan Amurka ta ayyana kasar Sin a matsayin mai leken asiri a duniya, saboda wata balan- balan da ya shiga sararin samaniyarta bisa kuskure, hakan yana nuna cewa ita ma kasa ce mafi son leken asiri a duniya ko a’a?
Fuska biyu da Amurka ke dauka a fannin tsaron kasa, yana da ban dariya sosai. Amma, shin ko wace kasa ce ta fi son leken asiri a duniya, ba shakka al’ummar duniya na da ra’ayinsu. (Mai zana da rubuta: MINA)