Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin za ta aiwatar da matakan da suka dace, domin shawo kan kalubalen da kasar Zambia ke fuskanta a fannin biyan bashin da ake bin ta.
Wang, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce kamata ya yi dukkanin masu ruwa da tsaki su fahimci gaskiya, su kuma amince da juna, tare da aiki tare domin bankado hanyar warware wannan kalubale. Jami’in ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da tattaunawa ta kusa, da shawarwari da Zambia, da sauran bangarorin da batun ya shafa, domin kaiwa ga warware batun bashin na Zambia. (Saminu)