A yau Talata ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kira wani taro, inda aka yi bayani kan yadda za a ingiza aikin farfado da kauyukan kasar daga dukkanin fannoni a bana.
Yayin taron, an bayyana cewa, an gudanar da ayyuka masu nasaba da aikin gona, da raya kauyuka, da manoma yadda ya kamata a kasar Sin a shekarar da ta gabata, lamarin da ya taimakawa ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma a kasar.
Alal misali, adadin hatsin da aka samu a kasar a bara, ya kai kilo biliyan 686.5, adadin da ya karu da kilo biliyan 3.7 bisa na shekarar 2021, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Kaza lika an ci gaba da tabbatar da sakamakon da aka samu wajen yaki da talauci, yayin da kudin shigar manoman kasar ya karu sannu a hankali, inda matsakaicin kudin shigar ko wanen manomi a duk shekara, ya kai sama da kudin Sin yuan dubu 20, adadin da ya karu da kaso 4.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
Bugu da kari, an ingiza fardado da kauyukan sassan kasar lami lafiya, tare kuma da ciyar da sana’o’in kauyukan gaba yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Jamila)