Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta karbi ‘yan Nijeriya 150 da aka kwaso daga Niamey da ke Jamhuriyar Nijar.
An karbe su ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
- Abin Da Ya Sa Muka Tsare Fani-Kayode -DSS
- Kin Bin Umarnin Kotu Kan Batun Canjin Kudi Zai Iya Kawo Koma Baya – Masana
Sun dawo ne a cikin jirgin Boeing 737-4B7 na Sky Mali mai dauke da lamba FMI 6001.
Jirgin wanda ya sauka da misalin karfe 11:20 na safe hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta kasa da kasa (IOM) ce ta shirya dawo da su.
Jami’in NEMA da ke Jihar Legas, Ibrahim Farinloye ne ya wakilci Darakta-Janar na hukumar, Alhaji Mustapha Ahmed don tarbar su tare da mara bayan wasu daga cikin jami’an hukomomin gwamnati.
Daga cikin wadanda aka dawo da su akwai matasa maza 98 da yara 11 da jarirai biyu da mata 24 da ‘yan mata 13.
Sauran hukumomin gwamnati da suka tarbe su a filin jirgin akwai Hukumar Kula da Shige da Fice da Hukumar Dakile Safarar Mutane (NAPTIP) da Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama da kuma jami’an rundunar ‘yansanda da sauransu.