Ƙungiyar Matasan Arewa Mazauna Legas, ta jaddada kira ga al’ummar arewa da cewa bai kamata yankin ya yi sakaci har ya koma gidan jiya ba dangane da halin ha’ula’in da aka jefa shi ciki na tashe-tashen hankula da ƙangin talauci da karayar tattalin arziki.
Ƙungiyar ta sake nanata kiran ne sakamakon abin da ta kira “yunƙurin wasu marasa kishin al’ummar yankin na sake mayar da shi gidan jiya domin biyan muradun ƙashin kansu a zaɓen 2023 da ke tafe”.
- 2023: Buhari So Ya Ke APC Ta Fadi Zabe – Ganduje
- Shirin Kawo Karshen Yi Wa Mata Kaciya Nan Da 2030
Ƙungiyar wadda ta yi kiran ta bakin shugabanta, Alhaji Ibrahim Yaro Galadanci, ta ƙara da cewa dangane da zaɓen 2023 musammam na shugaban ƙasa mun ji yadda wasu shugabanni daga arewa suke ɓaɓatu domin cikar burinsu na son zuciya, suna so a goyi bayan waɗanda za su ƙara kashe mana yanki, marasa riƙon amana, to muna faɗa wa mutanen arewa cewa wannan baa bin amicewa ba ne a gare su, sannan su kuma masu yi su san cewa komai nisan jifa ƙasa zai sauko.”
Ƙungiyar ta ci gaba da cewa tun daga dawowar mulkin dimokuraɗiyya ake wa yankin zagon ƙasa kuma idan har ba a farga a wannan lokaci na zaɓe ba, za a yi aikin da-na-sani.
“Domin lokaci ya yi da za mu zama tsintsiya maɗaurinmu ɗaya, wallahi tsakanin musulmin arewa da kiristocin arewa kowa ya sani tun a shekarar 1999 aka shirya kawar da dukkan ‘yan arewa daga doran ƙasa, aka dinga yi mana kisan gilla, ana ƙona dukiyarmu amma sabo da baragurbin shugabanni da suka mayar da mu saniyar ware, babu wasu masu ƙwatar wa ‘yan arewa ‘yanci. Duk inda ake rigima ɗan arewa ake kashewa, waye bai da masaniyar hakan a wannan lokacin.
“Dan haka muna kira da babbar murya, babu yaudara wallahi, lallai mu ƙwatar wa kanmu ‘yanci domin mafitarmu a yanzu shi ne haɗin kai mai ƙarfin gaske wanda dole mu samu sauyi da taimakon Allah, mu yi ƙoƙarin haɗa kan kwankwaso da Al-Musatapa domin arewa muna da makama. Duk arzikin da Allah ya shinfiɗa a ƙarƙashin ƙasa yana yankin arewa, tun daga kan Gold (Zinare) da manyan ma’adanai waɗanda ka da mu yi sake masu cewa su ne shugabaninmu su sayar da mu tun da sun kasance karnukan farautar waɗansu.” In ji shugaban ƙungiyar.
Har ila yau, ƙungiyar ta yi waiwaye adon tafiya game da manyan rikice-rikicen da ta ce an ƙirƙiro domin wargaza yankin, “masu haɗa waɗannan rigingimu da makirce-makice sun cire rahamar Allah a zukatansu, suka bari aka ƙirƙiro Boko Haram, aka ƙirƙiro rigimar manoma da makiyaya, saboda dukiyar da take Maiduguri da Yobe da Zamfara da Sakkoto da Neja da Kogi duk duniya babu ƙasar da za ta iya ja da arzikin da Allah ya yi mana, amma kuma ga mutanenmu suna cikin yunwa da talauci, don haka mu zaɓi ‘yan siyasa masu kishin al’umma da za su iya kawo gyara.”
Alhaji Ibrahim ya kuma nunar da cewa ba saboda wata jam’iyya ɗaya suke waɗannan kiraye-kirayen ba, yana mai cewa, “dan ba ma jam’iyya, abin da muke so mutanenmu na arewa su yi kawai, mu yi ƙoƙarin janyo hankulan `yan’uwanmu waɗanda suna cikin duhu da su dawo hanya domin mu ceci rayuwarmu, muna da arziki, don haka a daina yi mana kisan gillah. Sannan a yi ƙoƙarin daidaita tafiyar Majo Hamza Al-Musatapa da Kwankwaso, wallahi alheri ne a gare mu, dan Allah mu yi wa azzaliman tsofaffin shugabaninmu bara’a lokaci domin wannan ne lokaci mafi dacewa da za mu nema wa kanmu mafita.”
Wakazalika, ƙungiyar ta matasan arewa ta ce taron da gwamnonin Nijeriya suka yi da shugaban ƙasa a kan batun canjin kuɗi ba don talakawa suka yi ba, “taron da suka je Abuja suka samu shugaban ƙasa a fadarsa sabo da maganar canjing kuɗi domin kansu ne ba don talaka ba. Don su ma za su yi asara shi ya sa suka je, saboda mutum nawa aka sace a arewa ban da waɗanda aka yi wa kisan gilla, me ya sa babu wanda ya ce ya kamata su yi ƙungiya dan hakan? Lallai ya zama wajibi mutane mu farka mu yi wa kanmu ƙiyamullaili.” In ji Galadanci.