A daidai wannan lokacin da ake shirye-shiryen fara aikin noma na daminar bana, an yi kira ga gwamnatin jihar Inugu da ta tallafa wa manoman jihar, musamman da rance don kara bunkasa sanarsu da habaka tattalin arzikin jihar.
Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Inugu Romanus Ezeda ne ya yi wannan kiran a hirarsa da manema labarai a jihar.
- Da Dumi-Dumi: CBN Ya Musanta Bai Wa Bankuna Umarnin Karbar Tsoffin Kudi
- NEF Ga Buhari: Kar Ka Sake A Karkashin Mulkinka Ka Bari IPOB Ta Hana ‘Yan NIjeriya Kada Kuri’a
A cewar Romanus, noma babbar hanya ce da za a kara samar da ayyukan yi, mussaman ga matasa, inda ya ce, muna samun tallafin da ya dace tun daga matakin gwamnatin tarayya zuwa na jiha kadai ne, zai sa ‘ya’yan kungiyar su yi noman abincin da zai iya ciyar da ‘yan kasar nan.
Da yake yin tsokaci a kan noman bana musamman a jihar shugaba Romanus Eze ya shawarci manoma da cewa, kada su yi gaggawar shuka saboda fara saukar ruwan sama da wuri, inda ya kara cewa, wannan ruwan ba ya jika gona sosai.